TARO: Shugabanin kasashen duniya sun tattauna hanyoyin samar maganin rigakafi wa kowa da kowa

0

Shugaban majalisar dinkin duniya, UN António Guterres ya bayyana cewa baya ga sarrafa maganin rigakafi da aka maida hankali a kai za a kuma tabbatar da cewa idan an yi maganin ya isa ga kowa da kowa a duniya.

Guterres ya fadi haka ne a taron da gwamnatin kasar UK ta shirya domin samar wa mutane ingatattun da isassun maganin rigakafi domin kare su daga kamuwa da cututtuka musamman coronavirus.

Shugaban kasashen duniya da suka hada da firaya ministan kasar Canada Justin Trudeau, Sarkin kasar Jordan Abdullah bin Al Hussein, shugaban kasan Ethiopia Sahle-Work Zewde na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.

Taron ya tattauna hanyoyi samar da maganin rigakafi ga mutanen duniya musamman ga kasashen da ba su da karfin arziki.

Sannan shugabanin kasashen duniyan da suka hakarci taron sun sabonta alkawarin bada gudunmawar kudade wa kamfanin sarrafa magunguna na Gavi domin sarrafa ingantattun maganin rigakafi.

Sabonta alkawarin bada gudunmawar kudaden da shugabanin kasashen duniya suka yi zai taimaka wajen kara yawan maganin rigakafi da zai kai miliyan 300 domin kare kiwon lafiya yara daga yanzu har zuwa shekarar 2025.

Guterres ya yaba da kokarin da kamfanin Gavi ke yi wajen sarrafawa da tsara hanyoyin raba maganin rigakafin ga fuk kasashen duniya.

Ya ce Bincike ya nuna cewa akwai yara miliyan 20 da basu kammala yin allurar rigakafi ba a duniya.

Guterres ya ce daga cikin wannan yawa yaro daya cikin yara biyar bai taba yin allurar rigakafi ba.

Ya ce yara irin haka za su fuskanci matsalolin kiwon lafiya da dama musamman a wannan lokaci na coronavirus.

Guterres ya kuma tsaro wasu hanyoyi guda uku da za su taimaka wajen inganta yi wa yara allurar rigakafi.

1 – Farko dai kamata Ya yi a tsara hanyoyin da suka fi dacewa domin samar da isassun maganin rigakafi a duniya.

2 – Za kuma a iya maida hukumomin dake raba maganin rigakafi cibiyoyin kula da kiwon lafiyar mutane ya yin da suke raba maganin rigakafi.

3 – Sannan bayan an hada rigakafin cutar Covid-19 za a tabbatar kowa ya samu maganin a duniya.

Share.

game da Author