Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai jinkai
Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode Masa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa. Muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, kuma wanda Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Ya da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammadu (SAW), bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka, ya ku ‘yan uwa masu daraja, wani masani, mai hikimah yana fada a cikin wasu baitoci nasa masu cike da ilimi da hikimah cewa:
“Ana sa ran ko wace irin adawa ta kare, ta wuce, ta kwaranye, ta zama tarihi, a manta da ita, ta zamanto kamar ba’a yi ba, amma ban da adawar mutumin da yake adawa da kai saboda hassada, yace ita wannan adawa ba ta karewa har abada, matukar wanda ake yiwa hassadar yana raye, kuma yana ci gaba a rayuwarsa.”
‘Yan uwa masu girma, lallai idan muka dubi wadannan baitoci na hikimah, wallahi zamu ga cewa suna cike da ilimi da kuma gaskiya mai daci! Domin haka abun yake, in dai har ya kasance mutum yana adawa da kai ne haka siddan, babu wani dalili. Kawai yana adawa da kai ne saboda wata baiwa, ko wata daraja, ko wata daukaka da Allah yayi maka, to ban ga yadda za’a yi wannan adawa ta wuce ba, matukar kai da ake yiwa adawar kana nan cikin wannan daukaka da baiwa da ni’imah da Allah yayi maka.
‘Yan uwa na masu albarka, kowa yasan cewa na sha bayyanawa al’ummah cewa adawar da Gwamna Ganduje yake yi da Sarki Sanusi, wallahi adawa ce da ta samo asali daga hassadar da yake yiwa Sarkin, sanadiyyar daukakar da Allah yayi masa. A lokacin da nike fadar wannan magana, wasu suna ganin cewa ba gaskiya ba ne, to sai ga shi yanzu, alhamdulillah, muna raye, ya bayyana a fili karara cewa, abun da nike fadar ya tabbata gaskiya. Domin idan ba haka ba, a lokacin da Ganduje ya sha alwashin sai ya cire Sarki Sanusi daga sarauta, duk wani mutum mai mutunci da hangen nesa ya ja kunnen sa akan kar yayi haka, tun daga malamai da ‘yan siyasa, da manyan mu, da sauran su, amma ya ki ji, yaki ya saurare su, ya cire Sarki Sanusi. Bayan ya cire shi kuma, shi abun da yaso shine, ya ga Sarki Sanusi ya wulakanta, to sai Allah bai yarda da wannan mummunan nufi nasa ba, Allah ya kubutar da Sarki Sanusi, ya bar jihar Nasarawa ya koma birnin Legas. Tun a lokacin Ganduje yake ta yiwa Sarki Sanusi bita-da-kulli, a fili da kuma ta karkashin kasa, amma Allah yana dada kare shi daga dukkan wani abu da suka kulla.
Sannan duk duniya ta shaida hakuri da tawadu’u da tawakkali irin na Sarki Sanusi, domin duk wulakanci, da cin mutunci, da tozarci da suka yiwa Sarkin, suka cire shi daga gadon sarauta, sun zaci zai yi turjiya, yace bai yarda da sauke shi ba, ya tafi kotu, domin kalubalantar sauke shi din. To amma sai bai yi hakan ba, kuma ya dogara ga Allah tare da yin tawakkali gare shi, domin yasan shine mai yin komai. Kuma yayi jawabin goyon bayan wanda aka nada Sarki, kuma yayi kira ga dimbin magoya bayansa da masoyansa, cewa su goyi bayan wanda aka nada, kuma suyi masa fatan alkhairi, kuma yayi kira da kar wanda ya tada hankali, kuma alhamdulillah, an bi umurnin Sarki Sanusi akan wannan, kuma duk duniya ta shaida haka.
Sannan bayan wannan, tun da aka sauke Sarki Sanusi daga sarauta, babu wanda yaji yayi wata mummunar magana ga gwamnatin jihar Kano ko ga masarautar Kano. Ya manta da abun da ya faru, yaci gaba da harkokin sa.
Amma yanzu kwatsam, kuma sai muka ji Gwamna Ganduje yana cewa wai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano za ta ci gaba da binciken Sarki Sanusi. Ko akan meye? Oho!
Domin babban sakataren yada labaran gwamnatin jihar Kano, mai suna Abba Anwar, shine ya fitar da wannan sanarwa jiya litinin, 15/06/2020 wadda ya sanya wa hannu. A ciki ya tabbatar da cewa Ganduje ne ya fadi wannan a ganawar da yayi da ‘yan jaridu a sashen gidan Afrika da ke gidan gwamnatin jihar Kano, ranar litinin 15/06/2020 (wato jiya kenan).
Sannan labarin da muka samu daga majiya mai tushe, kuma kwakkwara shine, cewa an yi wani taro ne domin a lalubo kuma a zakulo duk wata hanya da za’a yi amfani da ita a kullawa Sarki Sanusi sharri, kuma a kama shi da wani laifi don a tozarta shi. Kuma wannan labari ya tabbatar da cewa, Gwamna Ganduje ne yake tursasawa shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano da yabi Sarki Sanusi da sharri, kuma ayi duk yadda za’a yi a zakulo wani laifin da za’a kama shi da shi, amma shi shugaban hukumar yana ja da baya, kuma yana dari-dari da lamarin, domin ya gano cewa jama’ah sun san cewa zaluntar Sarki Sanusi kawai aka yi, kuma bashi da wani laifi.
Ya ku ‘yan uwa masu daraja, abun tambaya anan shine, shin wai ba Gwamna Ganduje bane yake cewa Muhyi Magaji mutum ne mai cikakken ‘yanci, kuma wai yana cewa babu wanda yake sa shi ya binciki wani? To idan har abun da yake fada gaskiya ne, me yasa yanzu yake bashi umurnin ya binciki wani? Wannan ya nuna cewa kenan al’amarin duk siyasa ce kawai, kuma wannan ya nuna dama can shine yake sa su suci mutuncin mutane saboda wata manufa tasa ta siyasa.
Ya ku al’ummah, wallahi ku sani, duk wannan bita-da-kulli da suke yiwa Sarki Sanusi ba komai bane illa hassada. Domin idan ba haka ba, mutanen nan sun sauke shi daga sarauta, amma dai har yanzu ace sun ki su kyale shi, ba don komai ba sai don saboda dama can adawa ce ta hassada? Haba jama’ah! Wace irin al’ummah ce wannan da bamu nufin junan mu da alkhairi kullun, sai sharri?
Ya kamata dai mu sani, wallahi ita hassada ba ta da kyau, kuma wani mugun ciwo ne da ke nukurkusar mai yinta a cikin zuciyarsa shi kadai. Hassada ita ce jin zafi, daci, ko bacin rai a yayin da kaga wani dan’uwanka, ko makwabcinka, ko abokinka ko ma wani kawai da ka sani a duniya ya samu daukaka, ko wace iri ce. Kuma hassada ta kasu gida uku:
1. Akwai hassadar ganin kyashi, shine mutum yaji a zuciyarsa cewa don me wani zai fi shi wani abu a rayuwa; kudi, mulki, ilimi, daukaka ko kuma baiwa ko mukami ko wani matsayi.
2. Mutum yaji shi baya son kowa ya samu wani abun alkhairi ko wata karuwa sai shi kadai.
3. Mutum yaji cewa idan dai shi ba zai samu abu ba to gara kar kowa ya samu. Irin su sune suke yin a fasa kowa ya rasa. Kuma irin wannan hassadar tafi ko wace hassada muni da hadari.
Ya ku jama’ah, domin in fito maku da al’amarin a fili, don kowa ya fahimce shi, hassada ita ce ganin kyashi, ko nunkufurci, ko kiyayya. Kuma yawanci wanda ake yiwa hassada shine mutum mai abin hannu, ko mai ilimi, ko mai mulki, ko mai wani matsayi na addini ko na duniya. Kuma yawanci abin da yasa mutane suke yin hassada shine, rashin imani da tsoron Allah, rashin yarda da hukunci da kaddarar Allah, rashin kyakkyawan tunani, izza, ji-ji-da-kai, son girma, son shugabanci ko son nuna isa, da kazantar zuciya, mugunta, zalunci, rashin tarbiyyah da kuma mummunar dabi’a. Ina rokon Allah ya kare dukkanin Musulmi daga cutar hassada, amin.
Kuma hassada ita ce mutum yayi burin abin da ke wurin wanda yake yiwa hassadar na alkhairi, na abin duniya ne ko addini, ya gushe. Wannan haramun ne, domin yana cutar da jiki da addini. Allah, saboda Ya nuna tir din Sa da wannan dabi’a da masu yin ta, sai yace:
“Ko suna hassadar mutane ne a kan abin da Allah Ya ba su daga falalarSa…? [Suratun Nisa’i: 54]
Kuma Allah Mai girma da daukaka, Ya ja hankalinmu da neman tsari daga sharrin mai hassada, inda Yace:
“Da sharrin mai hassada, idan ya yi hassada.” [Suratul Falak: 5]
Kuma Manzon Allah (SAW), ya gargade mu kan matsalar hassada da irin illar da ke tattare da ita, a inda yace:
“Kashedin ku da hassada, saboda tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cinye kiraruwa.” [Abu Dawuda ne ya ruwaito shi]
Sannan kuma ana neman tsari daga mai hassada a lokacin da ya bayyana mummunar manufarsa ta yin hassadar, domin mai hassada yana iya yin komai domin ganin ya cimma burinsa na sharri da mugunta.
Daga karshe dai ya kamata duniya ta fahimci abun da yake faruwa. Wadannan mutane sun sha alwashin sai sun ci mutuncin wannan bawan Allah, wato Sarki Sanusi. Sun sauke shi daga sarauta, sun dauka cewa hankalinsu zai kwanta, amma tun lokacin da suka sauke shi hankalinsu dada tashi kawai yake yi kullun, kuma talakawa sun gano su, shine yanzu suke kokarin fito da wata hanya kuma, don su huce haushin su akan Sarki Sanusi.
To su sani, in Allah yaso ba zasu taba cimma burin su ba. Domin shi dai Sarki Sanusi ba ya da kowa sai Allah. Kuma bai riki kowa ba sai Allah. Duk kuwa wanda ya rike Allah, to cin nasara akan sa zai yi wahala.
Kuma wai ma wani abun mamaki shine, su mutanen nan, duk wannan hali da arewa ta ke ciki na rashin tsaro, da yunwa, da talauci, da cututuka, sam bai dame su ba. Domin idan ba haka ba, yaya za’ayi a lokacin da ake ta kokari da fadi-tashin ganin arewa ta samu mafita daga halin da take ciki a yau, a samu lafiya da zaman lafiya, a samu hadin kai da kwanciyar hankali, wai a lokacin ne wadannan miyagun mutane za su fito da wata magana, wai za’a ci gaba da binciken Sarki Sanusi, kuma ba don komai ba sai domin mummunar manufarsu ta siyasa! Kai ma ka san cewa, wallahi wadannan mutane basu nufin Kano da arewa da alkhairi!
Daga karshe ina rokon Allah, muna tawassali da sunayensa tsarkaka, ya tausaya muna, ya karbi tuban mu, ya azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa, zaman lafiya da ikon cin jarabawar sa a kan mu.
Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, ka azurta mu da cikakken tsaro a yankin mu na arewa mai albarka, da ma Najeriya baki daya, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah, Muhammad (SAW).
Ina rokon Allah ya kyauta, kuma ya kawo muna mafita ta alkhairi, kuma yayi muna maganin duk wani makiri, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.