SUNAYE: Sabbin shugabannin jam’iyyar APC na rikon kwarya

0

A ranar Alhamis ne jam’iyyar APC ta nada sabbin shugabannin kwamitin gudanarwar jam’iyyar bayan ganawa da kwamitin zartaswar jam’iyyar tayi wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta kwamitin ta rusa kwamitin gudanarwar jam’iyyar, ta nada tsohon sakataren ta kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya rike jam’iyyar.

A jawabin shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce daga yanzu ba za a zuba ida ana ganin wasu na neman yagalgala jam’iyyar sannan ba a yi komai a kai ba.

Buhari ya ce shawarar sa shine a rusa kwamitin gudanarwar jam’iyyar, a nada sabo da zai shirya zaben gangami na jam’iyyar.

Sannan kuma ya ce duk masu kararraki a kotu kan jam’iyyar ko wani dan jam’iyyar ya gaggauta janye wannan kara.

” Dole mu dauki wadannan tsauraran matakai domin ceto jam’iyyar daga rugurgujewa musamman a wannan lokaci da za mu tunkari zabukan Edo da Ondo.

Ga Sunayen sabbin mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar da aka nada.

1. Governor Mai Mala Buni (Yobe) Shugaba

2. Governor Isiaka Oyetola – Wakilin yankin Kudu Maso Yamma

3. Ken Nnamani – Wakilin Yankin Kudu Maso Gabas

4. Stella Okorete – Wakiliyar Mata

5. Governor Sani Bello – Wakilin Yankin Arewa Ta Tsakiya

6. Dr James Lalu – Wakilin Na’kasassu

7. Senator Abubakar Yusuf – Wakilin Sanatoci na Jam’iyyar

8. Hon. Akinyemi Olaide – Wakilin Majalisar Tarayya

9. David Leon – Wakilin Yankin Kudu Maso Kudu

10. Abba Ari – Wakilin Arewa Maso Yamma

11. Prof. Tahir Mamman – Wakilin Arewa Maso Gabas

12. Ismail Ahmed – Wakilin Matasa

13. Sen. Akpan Udoedehe- Sakatare

Share.

game da Author