SUNAYE: Dalibai 10 da suka cira tuta a jarabawar shiga Jami’o’i na 2020 – JAMB

0

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’oin kasar nan JAMB ta bayyana sunayen dalibai 10 cikin dubban da suka jarabawar da suka fi samun maki a jarabawar 2020 da aka yi.

Hukumar ta ce wadannan dalibai sun samu maki daga 352 zuwa 365 a jarabawar.

Biyu daga cikin daliban ‘yan jihar Anambra ne kuma sun samu maki 365 da 363.

Daga nan kuma sai wani dalibi daga jihar Edo da ya samu maki 359, mutum biyu daga jihar Ekiti sun samu maki 358 da 356.

Dalibai biyu kuma daga jihar Delta sun samu maki 359 da 352 sannan sauran daliban da suka maki masu yawa ‘yan asalin jihohin Ondo, Akwa Ibom, Kwara, Oyo da Ogun.

“A lissafe dai mutum 13 ne suka fi samun maki masu yawa a jarabawar, Wasu daga cikin su sun samu maki daidai daya da haka ya sa aka hada su wuri daya. Inji kakakin Hukumar Fabian Benjamin.

Benjamin ya ce daliban sun nemi su karanta darussan da suka hada da Industrial Production, Mechanical, Civil, Computer da Electrical Engineering.

Ya ce hudu Za su yi karatu a Jami’ar jihar Legas, biyu a Jami’ar Covenant, biyu Jami’ar Obafemi Awolowo sannan biyu a jam’ar Ilori sannan daya a Jami’ar jihar Kwara.

Ga sunayen daliban

1) Maduafokwa Egoagwuagwu Agnes -365

2) Nwobi Okwuchukwu David – 363

3) Ojuba Mezisashe Shalom – 359

3) Elikwu, Victor Chukwuemeka – 359

5) Adebola Oluwatobi Paul – 358

6) Gboyega Oluwatobiloba Enoch – 356

7) Ojo Samuel Oluwatobi – 355

7) Utulu, Jebose George – 355

9) Osom Akan Awesome – 353

10) Akakabota Fejiro Simeon – 352

10) Ogundele Favour Jesupemi – 352

10) Alatise Monsurah Bisola. – 352

10) Adelaja Oluwasemilore Daniel – 352

Dalibai 1,949,983 ne suka rubuta jarabawar JAMB na shekaran 2020 a kasar nan.

An fara jarabawar ranar 14 ga watan Maris zuwa 21 ga Maris.

A yanzu haka dalibai 612, 557 ne suka samu shiga jami’o’i daga cikin 1,949,983 da suka rubuta jarabawar bana.

Share.

game da Author