Sojoji sun afka wa gungun tawagar kwamitin dakile Korona na jihar Barno, mutum daya ya rasu

0

Sojoji a motocin yaki uku sun afka wa gungun tawagar kwamitin dakile yaduwar cutar Korona na jihar Barno da sanadiyyar haka suka mutum daya ya samu rauni wasu kuma da dama suka ji ciwo harda mace mai ciki.

Wannan aika-aika da sojoji suka yi ya auku ne a shingen da gwamnati ta saka a iyakar shiga garin Maiduguri. A wannan wuri jami’an gwamnati sun yi cirko-cirko suna aikin hana motocin matafiya daga wasu jihohi shiga garin Maiduguri a bisa dokar da aka saka na hana matafiya zirga-zirga zuwa wasu jihohi a dalilin cutar Korona.

Cikin jami’an gwamnatin dake wannan wuri akwai kwamishinan Shari’a na jihar, Kaka Shehu da wasu manyan jami’an gwamnatin Barno.

” Yau mungamu da cin mutunci karara daga Sojoji. Sun iso wannan shinge inda muke aikin kare kasa da jihar mu, suka kutsa da karfin tsiya suka yi ragaraga da shingen, Motar aiki da ke ajiye a gaban shingen bai tsira ba tare da jami’an tsaro dake ciki.

” Sojojin sun ragargaza motar da motocin su har ta wuntsila ta kife a kasa. Duka jami’an tsaron dake ciki sun samu rauni. Sannan kuma ba su tsaya nan ba suka yi awon gaba da Keke Napep dauke da fasinjoji har da mace mai ciki da wasu masu ‘yan babur dake gudanar da harkokin su.

Kaka Shehu Lawan ya kara da cewa a daidai sojojin na aikata wannan abin fargaba da tashin hankali, matafiya da aka tsare kuma suna ta jinjina musu suna zuga su su cigaba kawai domin su samu daman kutsawa cikin garin Maiduguri.

Mataimakin gwamnan jihar Barno Umar Kadafur wanda shine shugaban Kwamitin Korona na jihar Barno ya gaggauta garzayowa wannan wuri, sannan yayi tir da abin da sojojin suka aikata.

Ya kira kwamandan Sojoji na jihar domin sanar masa da abin da ma’aikatan sa suka yi.

Kwamandan ya shaida wa mataimakin gwamna cewa kwamandan da ya umarci sojojin su aiakta abinda suka yi shine, wai yaga dandazon matafiya ne tsare a wannan shinge, sannan da fargabar diran Boko Haram a wannan wuri shi yasa suka bude hanyar.

A karshe Kwamandan ya ce lallai rundunar za ta bi diddigin abinda ya faru kuma za a hukunta duk wadanda suka aikata haka.

Share.

game da Author