Sharudda da matakan karbar jinginar kananan rijiyoyin mai 57 a Najeriya

0

Hukumar Kula da Hako Albarkatun Danyen Mai (DPR), ta fito da wasu tsauraran sharuddan samun hakkin mallakar jinginar karamar rijiyar danyen mai a kasar nan.

Sanarwa ta bayyana cewa akwai kananan rijiyoyin danyen mai har guda 57 da Gwamnatin Tarayya za ta bayar jingina ga duk kamfanonin da suka cika sharuddan da DPR ta gindaya.

Sharuddan kamar yadda Shugaban DPR Sarki Auwalu ya rattaba hannu, sun hada da:

1. Sai kamfani mallakar ‘yan gurguzun ‘yan Najeriya, babu gauraye da dan wata kasa ko daya.

2. Ya kasance masu kamfanin na da sha’awar zuba jari da jimirin aikin hako danyen mai da hada-hadar kasuwancin sa.

3. Banda duk wani kamfanin da Gwamnatin Tarayya ke bi bashi bai biya ba.

4. Banda kamfanin da ya san zai fara ya kakare.

5. A sani cewa rijiyoyin akwai na cikin filayen kan tsandaurin kasa, akwai na cikin surkukin manyan hakukuwa, akwai kuma na bakin gefen teku.

Kudin Cika Ka’idojin Karbar Jingina:

1. Kamfani zai biya naira N500,000 ta yin rajista.

2. Sai kuma naira milyan 2 kudin na-gani-ina-so na kowace rijiya daya.

3. Akwai naira milyan 3 kudin shiga gasar mai-rabo-ka-dauka na kowace rijiya daya.

4. Sai dala 15,000 ladar tattara bayanai.

5. Sai dala 25,000 kudin sahale wa kamfanin yardar damka masa jinginar rijiyar mai.

6. Sai wata dala 50,000 kudin tabbatar da cewa kamfani ba-da-wasa-yake-ba.

7. Akwai kuma dala 25,000 kudin tattara wa kamfani bayanin sirrin zurfin rijiya da kintacen yawan albarkatun da ke kwance a karkashin rijiyar.

8. Za a bar kofa a bude tsawon watanni shida, duk kamfanin da ke bukatar cika fam, dai ya garzaya.

Cinikin Biri A Sama:

Wadannan rijiyoyi dai da ake talla, wato ‘Kananan Rijiyoyi’, filaye ne 57 da a baya aka taba bayarwa ga wasu kamfanoni suka fara hakar rijiyoyin mai, amma suka watsar.

Wasu sun watsar bayan shekaru goma ko kasa da haka, bayan sun gano albarkar danyen man da ke kwance a kasan rijiyar, bai kai darajar makudan kudaden da ake ksshewa wajen hako man ba.

Wasu kuma an fara haka, amma aka watsar saboda wasu dalilai.

Akwai kuma bukatar kowane kamfani ya aika da bayanan karfin sa, nagartar sa, irin harkokin da ya yi a cikin tsarin gaskiya da gaskiya da kuma karfin yawan ma’aikatan sa tare da irin matakan kula da lafiyar ma’aikata da kamfanin ke dauka.

Sai dai kuma wata kungiya ta nemi a bayyana sunayen wadanda suka mallaki duk wani kamfanin da aka bai wa rijiyoyin jingina.

Share.

game da Author