Saudiyya ta saka sabbin dokoki bayan samun karin wadanda suka kamu da Korona

0

Kasar Saudi Arabiya ta saka sabbin dokoki domin dakile yaduwar Korona da a baya ta sassauta bayan samun karin mutane da suka kamu da cutar.

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Saudiyya ta bayyana cewa bayan sassaiuta dokar yana walwala da bude masallatai da gwamnatin kasar tayi an samu karin mutane da suka kamu da cutar da yawa, hakan ya sa dole ta dawo da wasu dokokin domin kare mutanen kasar.

Idan ba a amanta kasar Saudiyya ta yarda a bude masallatai banda na harami a sassauta doka da tayi a baya.

Kasar Saudi ta zarce mutum 100,000 da suka kamu da cutar Korona tun bayan bullar cutar a kasar sannan mutum sama da 700 sun rasu.

Mutum sama da 400,000 suka mutu a sanadiyyar wannan cuta a duniya, kasar Amurka ce ta fi kowace kasa yawan wadanda suka mutu a dalilin wannan cuta.

Share.

game da Author