Yunkuri, kokari, gaganiya da muradin tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Tinubu na gadon kujerar shugaban kasa daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari a 2023, ya samu cikas da koma-baya, ganin yadda a rikicin da ya dabaibaye APC, Buhari ya goyi bangaren masu tsantsar adawa da Tinubu.
Tinubu dai shi ne bangon jinginar Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da aka dakatar. Kuma da shi din ne Oshiomhole ke tinkaho.
Tinubun da ‘yan APC ke kira “Jagoran Jam’iyya na Kasa”, ya ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar APC da kuma nasarar da ta samu a zaben shugaban kasa na 2015.
Duk da dai Tinubu bai fito ya bayyana muradin sa a fili ba, amma dai a fili ta ke cewa ana rade-radin ya na ta mafarkin zama shugaban kasa a 2023, bayan wa’adin Buhari na zango na biyu kuma na karshe ya kare a ranar 29 Ga Mayu, 2023.
A ranar Laraba Buhari ya fito baro-baro ya bayyana cewa ya na goyon bayan bangaren shugabancin riko na Victor Giadom.
Giadom ya yi amfani da umarni da hukuncin kotu ne ya ce shi ne shugaban riko na kasa na APC, bayan da kotu ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Tinubu.
Su kuwa wasu mambobin Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na APC, su 18, sai suka bayyana a ranar waccan Talata cewa sun nada Mataimakin Shugaba na Kasa da ke Shiyyar Kudu, Abiola Ajimobi, a matsayin Shugaban Riko.
Ranar Litinin kuma sai NWC din dai suka sauke Victor Giadom daga mukamin sa, suka nada Worgu Boms a madadin sa.
Sai dai kuma a cikin wata sanarwa daga hannun Kakakin Yada Labaran sa Garba Shehu, Shugaba Buhari ya ce shi dai ya na bayan Victor Giadom, domin shi ne hannun da doka ta nuna da yatsa a matsayin wanda ya dace a bi.
Su kuwa ‘yan bangaren Ajimobi, sai suka rika cewa taron Kwamitin Zartaswa da Giadom ya kira wanda Buhari ya ce zai halarta, haramtacce ne. Har ma suka rika jawo wasu ayoyin da suka ce sun haramta taron daga cikin kundin dokokin Najeriya.
Sakataren APC na Kasa Waziri Bulama, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa taron da Giadom ya kira ya kauce wa dokar jam’iyyar APC.
Tuggun ‘Yan Hana Ruwan Tinubu Gudu:
Akwai wasu gwamnoni bakwai da aka tabbatar sun rika kitsa kutunguilar rikici da Kwamitin Gudanarwa na Kasa, wanda aka hakkake cewa duk suna tare ne da ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
An ce gwamnonin bakwai sun hada karfi da Ministan Sufuri Amaechi.
Akwai Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, Atiku Bagudu na Kebbi, Simon Lalong na Filato, Nasir El-Rufai na Kaduna, Badaru Abubakar na Jigawa, Abubakar Bello na Neja da Mai-Mala Buni na Yobe.
Tinubu dai shi ne babban gogarman da ke goyon bayan Oshiomhole. Saboda haka ganin yadda Buhari ya goyi bayan wadanda ke kokarin tadiye kafafun Tinubu, hakan ya na nufin Shugaban Kasa ya watsa wa Tinubu kasa a cikin ido.
Sannan kuma wani abin da ake kira dukan-kabarin-kishiya da Buhari ya yi wa Tinubu shi ne, goyon bayan gugun gwamnonin da ke kokarin yi wa takarar shugabancin kasa na Tinubu ta-kife.
A ranar Laraba jajibirin taron APC, Gwamnan Kebbi Bagudu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa kokarin da gwamnonin ke yi shi ne su ceto jam’iyyar daga rudanin shugabancin da ta rufta.
“Yayin da Jam’iyya ta rufta cikin rikicin tulin kararraki a kotu, to ta shiga rudu sosai, wanda idan ba a yi gaggawar tsamo ta ba, to rugujewa za ta yi.”
Sai dai Bagudu ya ce su gwamnoni babu ruwan su day wani shiri ko kulli ko tuggun makomar 2023.