RIKICIN APC: Babu ruwan mu da Gaidom, Ajimobi ne shugaban APC na wucin gadi – Kwamitin gudanarwar APC

0

Mambobin kwamitin gudanarwar APC 15 cikin 21 sun rattaba hannu cewa Sanata Abiola Ajimobi ne shugaban Jam’iyyar na wucin gadi ba Victor Gaidom ba kamar yadda ya sanar a taron ‘yan jarida ranar Laraba.

Mataimakiyar jam’iyyar APC na shiyyar kudu-Maso-Kudu Hilliard Eta, a madadin sauran mambobin jam’iyyar ta ce gaba dayan su da suka saka hannu sun amince da Ajimobi ne zai rike jam’iyyar na wucin gadi.

Shugaba mai rikon kwarya, Ajimobi ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su maida takubban su. Cewa nan ba da dadewa ba zai kira taron iyaye da ‘yayan jam’iyyar domin warware wannan matsala da ake fama da shi.

Karanta labarin na baya:

Mataimakin sakataren jam’iyyar APC, Victor Gaidom ya nada kansa sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Gaidom ya ce shine kotu ta ba damar darewa kujerar shugabancin jam’iyyar, tunda kotun daukaka kara ta dakatar da Adams Oshiomhole.

” Dama tun a watan Maris babban kotu a Abuja ta yanke hukuncin nine shugaban jam’iyyar APC. A rashin shugaba, yanzu nine shugaba.

Sannan kuma ya soke zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamnan jihar Edo da jam’iyyar ta yi da ta hana gwamnan jihar Godwin Obaseki yin takara a jam’iyyar.

Ya ce kowa ya dawo a yi sabon zaben fidda gwani.

” Daga yanzu ba za mu sake barin ‘Yan tasha, gayyar sodi su shugabanci jam’iyyar mu ba. Saboda haka a matsayina ba sabon shugaban jam’iyyar APC, na soke zaben fidda gwani da aka yi a baya.

Rikicin APC da dakatar da Oshiomhole

A dalilin hukuncin kotu da ta dakatar da shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole daga ci gaba da zama shugaban APC kamar yadda babban kotu a farko ta yanke, jam’iyyar ta nada sanata Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo, ya zama shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya har sai kammala aiki akan shari’ar da aka shigar a gabanta.

Kakakin jam’iyyar APC, Mal Lanre Issa-Onilu ya ce dokar jam’iyyar ta ba mataimakin jam’iyyar na shiyyar Kudu damar darewa kujerar shugabancin jam’iyyar na wucin gadi a lokacin da aka samu gibi a kujerar shugabancin jam’iyyar.

Sanata Ajimobi, sirikin gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ne mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Kudu.

cikin hukuncin da kotun ta zartas, hatta jami’an tsaron dake kare shi duk an janye su. Kotu tace kotun baya ta yi daidai a hukuncinta. Ta yi watsi da korafin da Oshiomhole ya mika gabanta.

Idan ba a manta ba kotun a Abuja ta dakatar da Oshiomhole daga ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC a watan Maris.

Wanda ya shigar da karar Lauya Afolabi ya ce babban hujjan su na shigar da Kara shine an dakatar da Oshiomhole daga jam’iyyar a mazabarsa da gundumar da.

Yace hakan ya tabbatar da Oshiomhole ba Dan jam’iyya bane a yanzu saboda haka bai cancanci ci gaba da zama a kujerar shugabancin jam’iyyar ba.

Sai dai ko a a wancan lokaci, wata kotun Mai karfin iko irin na Abuja, a Kano ta ya ke hukuncin wancakalar da dakatar da Oshiomhole da kotun Abuja ta yi.

Oshiomhole ya garzaya kotun daukaka Kara domin kalubalantar wannan dakatar da shi da kotu ta yi da kuma garkame ofishin jam’iyyar da hukumomin tsaro suka yi wai suna yin biyayyane ga hukuncin kotu.

Share.

game da Author