RIKICIN APC: APC ta dauko hanyar rugujewa tun yanzu a rashin sahihin shugaba – Jigo a Jam’iyyar

0

Shikenan ga dukkan alamu dai jam’iyyar da ba a taba yin irinta ba a tarihin Najeriya, wato jam’iyyad da ta kada da jam’iyya mai mulki, jam’iyyar da koka bi ko abi maka dole.

Jam’iyyar ta lunkume, jar hula, koriyar hula, farar hula da bakar hula duk sun yi nitso cikinta gudun kada zanin su ya kwance a kasuwa a 2015.

Wani jigo a jam’iyyar wanda shine Direktan sakatariyar kungiyar gwamnonin jihohin da jam’iyyar APC ke mulki, Salihu Usman, ya bayyana a wata takarda da ya fitar ranar Alhamis, yana mai cewa, a halin rashin sahihin shugaba da jam’iyyar ta samu kanta a ciki yanzu, nuni ne cewa APC fa kila lokaci yayi.

” Haba dai, abu kamar babu kundin tsarin yadda za a tafiyar da jam’iyyar? Ko kuma dai kawai an yi watsi da ita ce kowa ya ci karen sa ba babbaka ne, kuma wai ace jam’iyya mai mulki kenan. Abin akwai daure kai.

” Ina Tinubu da Buhari ne wanda sune iyayen wannan jam’iyya, abin yafi karfin su ne ko kuma dai kowa ya kama gaban sa ne. Akwai dai alamun haka ganin halin da jam’iyyar ta afka ciki, sannan babu wani daga cikin su da yace in ta tafasa sauke.

Idan ba a manta ba, jam’iyyar APC dai yanzu tana kan keken makaho ne, sai abinda yayi mata birki.

Kotu ta dakatar da shugaban ta Adams Oshiomhole, wanda ya dare kujerar na kwance a asibiti ba lafiya, sannan wani can kuma ya kaddamar da kansa, shugaba jam’iyyar.

Share.

game da Author