RIKICIN AISHA DA SABIU: Ana binciken harbin bindiga da aka yi a fadar shugaban kasa – Garba Shehu

0

Idan ba a manta PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo muku labarin yadda ta kicime tsakanin uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da hadimin Buhari Sabiu Yusuf.

Rikici ya barke ne bayan Aisha ta umarci Sabiu ya fice daga fadar shugaban kasa ya je ya killace kansa bayan ya dawo daga tafiya da yayi wajen Abuja.

Sabiu ya shaida mata cewa ba zai killace kansa ba domin shugaba Buhari ya na bukatar sa.

An yi ta kai ruwa rana a tsakanin Aisha da Sabiu da ya kai ga an tsare masu kare Uwargidan shugaban kasa sai da Aisha ta sa baki.

A ranar Lahadi an ji karar harbin bindiga a fadar shugaban kasa.

An gano cewa a dalilin sabani da Aisha ta samu da Sabiu yau ADCn ta Shugaba ya harba bindiga a fadar shugaban kasa a kokarin sa na kare Aisha Buhari da nuna gwaninta.

Fadar shugaban kasa ta hanyar kakakin ta Garba Shehu ya ce za a gudanar da bincike kan wannan harbi da aka yi fadar gwamnati Sannan kuma ya yi kira ga ‘yan Najeriya kowa ya kwantar da hankalinsa cewa shugaba Buhari na nan cikin koshin lafiya kuma cikin tsaro mai nagarta.

Karanta labarin mu na baya:

Uwargidan shugaban Kasa Aisha Buhari ta koka da kakkausar murya yadda aka yi awon gaba da ADCn ta da jami’ai masu kare ta aka garkame su ba tare da an sanar da ita ba.

Aisha ta ce ” Yanzu dai na kira sufeto janar din ‘Yan sanda domin a saki masu kare da aka garkame a kurkuku domin kare su daga hadarin kamuwa da cutar COVID-19.

Cikin wadanda aka tsare, akwai ADCn Aisha, Usman Shugaba da da wasu masu kare uwargidan shugaban kasan.

Bayanai sun nuna cewa akwai yiwuwar an tsare wadannan masu kare uwargida Aisha ne bayan cacan baki da ita kanta ta yi da wani daga cikin hadiman shugaba Buhari saboda tilasta wa wani hadiminta ta ya killace kansa bayan ya dawo daga tafiya.

Shidai ADCn Aisha yayi tafiya ne sannan bayan ya dawo sai aka shawarce shi da ya killace kan sa na kwanaki kafin ya shigo fadar shugaban kasa. ADCn ya banzatar da wannan gargadi ya ci gaba da zuwa aiki.

Daga nan sai maganan ya koma kunnen Aisha, ita kuma ta tunkari wannan hadimin shugaban kasa inda suka kaure da cacancan baki, wasu daga cikin masu kare ta suka saka baki nan take suma.

Kakakin Aisha Buhari, Aliyu Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari inda ya ce ba a kyauta wa uwargidan shugaban kasa ba tsare masu kare ta kai tsaya ba tare da ta sani ba.

” Ya dai kamata a ce kafin a tsare wani mai kare matar shugaban kasa, annsanar da ita tukunna, ba kawai a yi awon gaba da ita ba, ita kuma ko oho.

Abdullahi ya ce ba a yi abinda ya dace kuma ba a daraja ofishin ta da matsayinta na maidakin uwargidan shugaban kasa ba.

Share.

game da Author