RASHIN TSARO? Allah Sarki Arewa, Daga Gambo Lawal

0

Babban dalilin da ya sa mutanen yankin Arewacin Najeriya suka nuna wa gwamnatin Goodluck Jonathan kiyayya karara tun daga 2011 bai wuce saboda tsanannin rashin tsaro da ake fama da shi a yankin ba musamman matsalar hare-haren Boko Haram.

Mutane da dama sun gama yanke hukuncin cewa cewa lallai wannan hare-hare makarkashiyace da aka shirya don kassara Arewa a wancan lokaci.

Jama’a sun rika yin Allah-wadai da wannan mulki na PDP sannan an yi rokon Allah ya kawo wa Najeriya sauyi ko don Arewa ta zauna lafiya.

A 2015, sai Allah ya kawo wata goguwar siyasa, goguwar da ba a taba yin irin ta ba a tarihin siyasar Najeriya. Goguwar da aka yi wa take ” In Baka Yi Bani Wuri” Kowa yabi aka hada kai, aka hada karfi, aka jingine da adawar yanki, kabilanci aka taru wuri daya tamau aka wancakalar da shugaban mai ci, shugaba Goodluck Jonathan na jam’iyyar PDP.

Haka yana gani ya hakura babu yadda zai yi, aka rantsar da sabuwar gwamnati.

‘Yan Najeriya kuma kowa cike fam da buri. Baba Buhari ya ci zabe, shinkafa zata dawo naira 100 mudu daga naira 230. Man fetur zai sauko, Tsaro zai tabbata musamman a Arewa, Boko Haram kuma kashin su ya bushe.

Tafiya tayi tafiya kamar za a kamar baza a ba, sai ayyukan garkuwa da mutane ya bullo gadan-gadan a yankin Arewa, da hatta janar din Soja, sai dai yabi jirgin Kasa ya tafi Abuja daga Kaduna amma ba wai ya bi hanya da mota ba. Sai gashi ana rige-rigen siyan tikitin jirgin Kasa da Sanatoci, manyan jami’an gwamnati gwamutse da talakawa, duk saboda tsoron mutuwa ko kuma wani dan karamin yaro ya rika sharara maka mari.

Wannan tashin hankali bai tsaya nan ba a kwana a tashi sai kuma aka fara bi gida-gida ana dauke mutane, abi mutum gona a dauke shi, mata mai dakan gero a kauye a hauro ta katanga a dauke ta, yara a makarata ba su tsira ba, kai hatta jami’an tsaro sai abi a dauke a ce sai an biya miliyoyin kudin fansa kafin a sake su, kai jama’a!

A kwana a tashi sai Jihohi irin su Kaduna, Zamfara, Niger, Kogi, Sokoto, Katsina suka zama shiga da alwalanka.

Ba a yin mako daya cur baka ji an kai hari nan ba ko can a wadannan jihohi, malam abu kamar almara.

Su ko jihohin Arewa maso Gabas sai abinda yayi gaba. Boko Haram sai su tare hanya su kashe mutane, su tafi har Bariki su kashe sojoji babu kakkautawa abin dai kamar a fim.

A yan kwanakinnan abin sai kara gaba yake duk da mutane na fama da tsanani da ukubar da aka saka musu da kuma aka fada saboda annobar KoronaBairos mahara da ‘yan bindiga basu daina kai farmaki garuruwa suna kashe muatane ba sannan suna sace dukiyoyin su.

A kullum za ka ji gwamnati na cewa ana samun nasara. A wasu lokuttan ma tun kafin su rufe bake zaka ji rahotan an kashe mutun 50 a can 70 a can abu dai kamar kowa yanzu yayi ta kan sa ne.

A wancan karon lokacin mulkin PDP, wasu daga cikin masu yin adawa ga gwamnatin da yin suka da yadda ake tafiyar da harkokin tsaro a kasar a lokacin, suna gwamnati yanzu wasu ma gwamnoni ne amma ba aji su sun fito suna kokawa kan yadda ake tunkarar tsaro a kasar ba. Kullum dai sai dai kaji ana samun nasara a harkar tsaro, Abin tambaya shine a ina ake samun nasarar?

Share.

game da Author