Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya, wato National Open University of Nigeria (NOUN), Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya yi kira ga sababbin ɗaliban jami’ar da su tashi tsaye wajen tunkarar duk wani ƙalubale da za su fuskanta a nan gaba, ciki kuwa har da ƙoƙarin magance cutar korona da ta addabi duniya a yau.
Ya yi wannan kiran ne a wajen biki na 19 na rantsar da sababbin ɗaliban da jami’ar ta ɗauka, wanda aka gudanar ta hanyar intanet a ranar Asabar ɗin nan, 13 ga Yuni, 2020.
A jawabin sa ga sabbin ɗaliban, su sama da 15,000, wanda ya karanta ta hanyar manhajar Zoom, Farfesa Abdalla ya yi kira a gare su da su ɗauki duk wani ƙalubale da su ka ci karo da shi a lokacin karatun su a matsayin tubalin gina rayuwar su.
Ya ce: “Da tubali ɗaya bayan ɗaya za ku iya gina katafaren gini, kuma kun hau kan hanyar cimma wannan nasarar domin kuwa burin ku na yin karatu shi ne ke iza ku.”
Mataimakin shugaban ya yi la’akari da cewa a yayin da wasu ɗaliban da dama su ke kallon shiga babbar makaranta a matsayin hanyar da za su sami kwalin da za a ɗauke su aiki, su kuwa sabbin ɗaliban jami’ar ta NOUN da dama ma’aikata ne ko masu sana’o’i.
Farfesa Abdalla ya ce yanzu da ayyukan ƙere-ƙere na fasaha su ka zama ruwan dare, jami’ar NOUN ta ƙarfafa amfani da hanyoyin yanar gizo ta yadda ɗalibai za su iya tuntuɓar malaman su kai-tsaye daga duk inda su ke.
Ya yi nuni da cewa jami’ar sa ita kaɗai ce ta kafa sashen samar da ababen karatu ta yanar gizo wanda a nan gaba zai iya rikiɗa zuwa jami’ar intanet mai zaman kan ta.
Ya ƙara da cewa a yanzu dukkan kwasa-kwasan da NOUN ke karantarwa su na da cikakkiyar amincewar Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa, wato NUC, ba domin komai ba sai don tabbatar da sahihancin su.
Ya ce: “Dukkan kwasa-kwasan mu da tsare-tsaren tabbatar da inganci da kuma hanyoyin karatun mu sun ma fi na wasu jami’o’in da aka saba zuwa, waɗanda su kan zo wajen mu don su ga yadda mu ke bi mu na samun wannan nasara ta ban-mamaki a fagen fasaha.”
Farfesa Abdalla Uba Adamu ya kuma sanar da sabbin ɗaliban cewa wannan bikin ƙyanƙyashe su ɗin shi ne na ƙarshe da ya gudanar a matsayin mataimakin shugaban NOUN, domin kuwa wa’adin aikin sa na shekara biyar zai ƙare ne a watan Fabrairu, 2021.
Don haka ya ce, “Ina so in sadu da ku nan da shekara huɗu masu zuwa a wajen bikin saukar karatun ku, ba a matsayi na na mataimakin shugaba ba, sai dai a matsayin baƙo da aka gayyata, in zo in same ku cike da ilimi da kuma cikakken shirin tunkarar rayuwa a saboda karatun da ku ka yi a NOUN, in yi alfaharin ganin kun samu sakamako mai kyau fiye da na kowane ɗalibi da ya kammala jami’a.”
Magatakardan jami’ar NOUN dai, wato Mista Felix I. Edoka, shi ne ya rantsar da ɗaliban, shi ma ta hanyar yanar gizo.
An kammala bikin ana musayar wasa da dariya a tsakanin mataimakin shugaban jami’ar da sababbin ɗaliban, waɗanda sun shiga bikin ta intanet ne daga sassa daban-daban na Nijeriya.
Haka kuma an watsa bikin kai-tsaye ta kafofin soshiyal midiya irin su Facebook da kuma hanyoyin intanet na NOUN.
A bikin dai babu irin ruguntsimin da aka saba gani, kamar saka tufafin jami’ar da ɗaukar hotuna, domin an yi komai ne daga gida saboda zaman kare kai daga cutar Covid-19 da ake yi tun lokacin da Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantu a watan Maris da ya gabata.
Jami’ar NOUN dai ita kaɗai ce irin ta a Nijeriya inda ake yin karatu daga gida, kuma ta fi kowace jami’a girma a yankin Afrika ta Yamma domin kuwa ta na da ɗalibai da su ka yi rajista da ita kimanin 580,000 waɗanda ke karatu a ofisoshin jami’ar guda 78 da ke sassan Nijeriya.
Darektan yada labarai na jami’ar, Ibrahim Sheme ya sa hannu a wannan takarda.