A rahotan bin ba’asin yadda ake gudanar da ayyuka a matatar man Kaduna da sauran kamfanonin mai mallakar kamfanin mai na kasa, NNPC, matatar man Kaduna bata iya tara ko sisi ba a shekarar 2018 sai ma kudi da aka kashe mata har naira biliyan 64.
Haka kuma rahotan ya nuna cewa ba a a shekara 2017, ta iya tara naira biliyan biyu ne kacal amma kuma an kashe mata sama da biliyan 112 na babu gaira bau dalili.
Matatar man Kaduna: An kashe naira miliyan N447.7 wurin yin tirenin din ma’aikata sanin makamar aiki, An kashe naira miliyan N230 domin samar da tsaro, Kayan sadarwa naira miliyan N37.3, ayyukan kai komo da kuma naira N843.
Bayan haka kuma an kashe zunzurutun kudi har naira biliyan 23 a cikin shekarar 2018 wajen biyan manyan darektocin ma’aikatar, albashin su, Alawus, da kudaden mutuwa da sauran su.
Idan ba a manta ba, shugaban kamfanin mai na Kasa Mele Kyari ya bayyana cewa gwamnati ba za ta a iya ci gaba da rike kamfanoni da matatun mai na kasa ba. Cewa za a mika su ga wadanda zasu iya gudanar da su ne.
A kamfen din 2019, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban Kasa a lokacin, ya bayyana karara cewa idan ya zama shugaban kasa zai saida matatun man kasar cewa hasara kawai ake yi maimakon amfana da su.