OBASEKI: Ku saurari inda muka dosa tunda APC ce ba ta yi da mu a Edo – Shugaban APC na jihar Edo

0

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Edo ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar musamman na bangaren gwamna Godwin Obaseki cewa su kwantar da hankalin su cewa nan ba da dadewa ba gabadayan su za su fadi inda suka dira.

” Abinda na ke so kowa ya sani shine, APC ce bata so muyi takara a karkashin ta, amma ai hakan ba zai hana yin takara ba. Saboda haka za mu gana a tsakanin mu sannan mu sanar muku inda muka dosa bisa irin hukuncin da muka yanke.

Akwai rade-radin cewa Obaseki zai koma jam’iyyar PDP ne.

Tun ana yi ana hasashen siyasa ce, wata rana za a dinke barakar dake tsakanin gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki da shugaban jam’iyyar APC, Adam Oshiomhole, yanzu dai an karkare tas.

Idan ba a manta ba da tsakar ranar Juma’a kwamitin dake tantance ‘yan takarar gwamnan jihar Edo na jam’iyyar APC suka ki tantance gwamnan jihar Obaseki cewa a kwai lauje cikin nadi a takardun karatun sa.

Hakan ya sa kwamitin ta ce bai ma cancanta yayi takarar gwamnan jihar ba saboda haka ba za ta tantance shi ba.

Daga nan sai aka tsame shi daga cikin wadanda za a tantance aka wancakalar a gefe.

Sai dai kuma bayan ambata haka da jam’iyyar ta yi, sai gwamna Obaseki ya fito karara ya ce ba zai kalubalanci hukuncin jam’iyyar ba, yana mai cewa tunda haka jam’iyyar APC take so ta ci gaba da gudanar da ayyukanta karkashin shugabancin Adams Oshiomhole dake yin mulkin kama karya, ta ci gaba amma shi ba zai yi jayayya da hukuncin da jam’iyyar ta yanke ba game da hana shi takara.

Kakakin Obaseki ya shaida wa manema labarai cewa dama kuma sun san da wannan wannan makirci da uwar jam’iyyar ta me kitsawa kafin ta bayyana haka.

” Muna sane dama cewa za a yi hakan tunda tun farko ba a so mu da mu ci gaba da zama a kujerar mulkin jihar ba. Shugaban jam’iyyar APC ya zama gwanki mai taka kowa. Yana yin mulkin Kama karya a jam’iyyar da aka tsara ta akan tabarmar adalci da manufofi domin inganta talakawa, sai gashi Oshiomhole ya wargaza ta dai-dai yanzu.

Obaseki ya kara da yin kira ga magoya bayan sa da su kwantar da hankalin kan abinda ya faru kuma su saurari shawarar da gwamnan zai yanke nan ba da dadewa ba.

Share.

game da Author