NAJERIYA: Yadda masana tattalin arziki suka sabule wa Kasafin 2020 wando a kasuwa

0

Masana tattalin arziki masu nazarin-kwakwaf da ke karkashin Kungiyar Leken Asiri da Bin Diggigin Kudade (SBM Intelligence), sun fallasa cewa ba gaskiya ba ne da ake cewa Kasafin 2020 na naira tiriliyan 10.8 ya fi duk wani kasafi yawa da daraja tun daga 1999 zuwa bana.

SBM Intelligence sun ce hanya daya tilo ta auna darajar kasafin kudi, ita ce auna kasafin wanda ake yi da takardun kudaden naira, sai a aza adadin kudaden a kan sikelin darajar dalar Amurka.

A kan haka ne SBM Intelligence ta ce idan ana maganar darajar kasafin kudi, to na shekarar 2013 ya fi na 2020 daraja sosai.

SBM ta ce faduwar darajar naira ya sa kasafin 2020 ya fuskanci zubewar daraja, kamar yadda kungiyar ta yi bayani dalla-dalla a kasa.

“Kasafin 2020 na naira tiriliyan 10.8, bai kai darajar kasafin 2013 wanda aka yi a kan naira tiriliyan 4.99 ba.

“Saboda kasafin 2020 ya tashi a kan dala bilyan 28 a farashin dala daya daidai da naira 361 farashin gwamnati. Kuma naira 430 a farashin kasuwar-tsaye.

“Shi kuwa kasafin 2013 na naira tiriliyan 4.99, ya tashi daidai da dala bilyan 31.5 a farashin gwamnati, kuma daidai da dala bilyan 30.6 a farashin kasuwar-tsaye.”

A kan haka ne SBM Intelligence ta ce kuskure ne a rika zuguguta kasafin 2020, har ana cewa ba a taba yin kamar sa ba daga 1999 zuwa bana.

“Ko kasafin 2019 na naira tiriliyan 10.33 da aka dauka, za a fahimci cewa ya kai kwatankwacin dala bilyan 28.7 a farashin naira kan dala 306.8 farashin gwamnati da kuma naira 359.8 duk dala daya a farashin kasuwar-tsaye. Saboda a wadancan lokutan duk dala ba ta yi tashin gwaron zabo ba kamar 2020 a yanzu.

“An dora darajar kasafin kudi da dala Amurka ce, saboda duk kayayyakin da gwamnati ko masu kwangilolin ayyukan gwamnati ke shigowa da su, duk da dala ake yin hada-hadar su a kasashen waje, ba da naira ba.

Kasafin 2020 dai ya hadu ga gagarimar matsalar da ta hada da barkewar cutar Coronavirus, wadda ta tsayar da dukkan hada-hadar tattalin arziki a fadin duniya.

Sannan kuma ta karya farashin danyen man fetur, ta yadda sai da aka kwashe tsawon lokaci ana neman mai saye, amma an rasa.

A Amurka sai ta ta kai ko kyauta aka tunkari manyan dillalan danyen mai aka ce su kwasa, babu yadda za su yi da shi. Dalili, kudin lodi da kudin ajiya a rumbunan danyen mai, su kan su jidali ne.

Najeriya dai da kudin danyen mai ta ke yi kasafin kudi tare da yin kirdadon kasafin a bisa farashin danyen mai.

Cikin watan Nuwamba, 2019, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kasafin kudin 2020 a kan gangar danyen mai daya dala 57.

Tuni wannan lissafi ya kwance, wanda masana su ka je igiyar gugar kasafin ta tsinke, gugar kuma ta fada rijiya, wato farashin danyen mai ya fadi kasa warwas.

Share.

game da Author