Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 566 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litinin.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litinin sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 166, Oyo – 66, Delta – 53, Ebonyi – 43, Plateau – 34, Ondo – 32, FCT – 26, Ogun – 25, Edo – 25, Imo – 15, Bayelsa – 13, Benue – 12, Gombe – 11, Kano – 11, Kaduna – 11, Osun – 8, Nasarawa – 7, Borno – 5, Katsina – 2 and Anambra – 2.
Yanzu mutum 25, 133 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 9,402 sun warke, 573 sun rasu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum, 10, 310 , sai kuma babban birnin tarayya Abuja – 1,818, Oyo – 1, 372, Kano – 1, 211, Rivers – 1, 056, Edo – 986, Delta – 965, Ogun –807, Kaduna – 703, Katsina – 549, Bauchi – 500, Gombe – 503, Borno – 491, Ebonyi – 481, Plateau – 405, Jigawa – 317, Imo – 318, Abia – 302, Enugu – 261, Ondo – 308, Kwara – 217, Nasarawa – 213, Bayelsa – 211, Sokoto – 151, Osun – 124, Akwa Ibom – 86, Adamawa – 84, Niger – 84, Kebbi – 76, Zamfara – 76, Anambra – 73, Yobe – 59, Benue – 59, Ekiti – 43, Taraba!- 19 and Kogi – 4.
Idan ba a manta gwamnatin tarayya ta janye dokar hana tafiye-tafiye a fadin kasar nan sannan ta bada umarnin a bude makarantu don ‘yan ajin karshe su koma makaranta.
Dokar zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuli 2020.
Bisa ga dokar gwamnati ta amince wa mutane su yi tafiya da a kokuttan da babu dokar hana walwala.
Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 Boss Mustapha ya Sanar da haka a taron ta da manema labarai a Abuja.
Ya ce gwamnati ta bude makarantun ne domin daliban da ke ajin karshe su fara murrajia da kuma shirin yin jarabawa.
Bayan haka Mustapha ya kuma ce gwamnati ta kara makonni hudu a karo na biyu na dokar dakike yaduwar cutar Korona a fadin kasar nan.
Karin zai fara aiki ne ranar 30 ga watan Yuni zuwa 27 ga watan Yuli 2020.
Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Afrilu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sassauta dokar zaman gida dole a karon farko da ya yi tsawon makonni biyar a Abuja da jihohin Legas da Ogun.
Dama kuma gwamnati ta sanar da cewa daga wannan mako za ta fi maida hankali a kananan hukumomin da cutar ta fi tsanani ne.
Ya ce a wadannan kananan hukumomi za a saka dokoki da zai sa a tunkari wannan annoba ta hanyar tsananta gwaji da samar musu da kula.