Hukumar Jami’oin kasar nan ta amince wa jami’o’i 12 kacal su rika gudanar da karatun nesa da dalibai da ake kira (Open Distance Learning, ODL)
Wannan sanarwa ya fito daga ofishin hukumar ne a ranar laraba inda ta ce cikin Jami’o’in da suka nemi a amince musu su rika yi 12 ne kacal suka cika sharuddan da hukumar ta saka.
Kakakin hukumar Ibrahin Yakasai ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa abinda ya sa jami’o’i 12 ne kacal suka cika sharuddan ya hada da karfin iya gogayya da fasahar zamani da ba kowani jami’a bace za ta iya.
” Shi karatun jami’a a yanar gizo ba irin na tattaunawar manhajar Whatsapp ko Telegram bane. Karatun na bukatar fasahar zamani gogewa a harkar ilimi wanda jami’o’in da aka zaba sun cika sharuddan. Za su karatu ta yanar gizo da ya hana da ganawa da malami kaitsaye da kuma karatu a makaranta tare da kow da kowa.
Ya kara da cewa ita jami’ar NOUN ta samu lasisin yin karantarwa ta yanar gizo ne kawai amma wadannan duka biyu za su rika yi.
Jami’o’in sun hada da
Ahmadu Bello University – Federal University
University of Abuja – Federal University
University of Maiduguri- Federal University
Modibo Adama University of Technology – Federal University
Obafemi Awolowo University – Federal University
University of Lagos – Federal University
University of Ibadan – Federal University
University of Nigeria – Federal University
Federal University of Technology, Minna – Federal University
Lagos State University – State University
Ladoke Akintola University of Technology – State University
Joseph Ayo Babalola University- Private University