Najeriya na neman karin Sojoji domin tunkarar Boko Haram – Zulum

0

Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum yayi tsokaci kan wasu muhimman dalilai da suka sa har yanzu Najeriya ta kasa gamawa da Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas.

Zulum ya fadi haka ne da yake maraba da tawagar sanatocin da suka zo yi masa jajen kisan mutanen da Boko Haram suka yi a ‘Yan kwanakinan a jihar.

Bulaliyar majalisar, Orji Kalu, tsohon gwamnan jihar Kashim Shettima da wasu sanatoci biyu dake wakiltan shiyyoyi a jihar Barno na daga cikin tawagar da suka ziyarci gwamna Zulum.

A bayanin da ya yi gwamna Zulum ya ce rashin isassun sojoji na daga cikin matsalolin dake kawo wa Najeriya cikas wajen gamawa da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Sannan yayi kira ga sanatocin su binciki
rashin kudi da sojojin ke kuka da su cewa yana kawo musu cikas a ayyukan su.

Zulum ya ce Najeriya ba Za ta iya gamawa da Boko Haram ba idan ba ta hada kai da kasashen dake kewaye da ita ba.

A karshe ya mika godiyar sa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kokarin da yake yi don a samu zaman lafiya a jihar tun 2015.

Tawagar majalisar dattawan sun jajanta wa gwamnan sannan sun bayyana cewa za su ci gaba da mara mata baya domin samun nasara a abubuwan da ta sa a gaba.

Share.

game da Author