Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa Najeriya na gab da samun shaidar rabuwa kwata-kwata da cutar shan-inna a Nahiyar Afrika.
Ofishin WHO dake Brazzaville a kasar Kongo ta sanar da haka a shafinta na Twitter ‘@WHOAFRO’.
WHO ta ce Najeriya ta kai ga Wannan matsayin ne a dalilin gamsuwar da Kungiyar yaki da cutar shan inna (POLIO) na kasashen Afrika (ARCC) ta yi game da ingancin kokarin kawar da cutar da gwamnatin kasar take yi.
Shugaban Hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) Faisal Shu’aib a shafinsa na twitter ‘@drfaisalshuaib’ ya bayyana farin cikin sa kan wannan nasara da aka samu.
Najeriya ta yi nasara a haka ne a dalilin namijin kokarin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi da dinbbin tallafin da kasar ke samu daga gidauniyar Bill da Melinda Gates da gidauniyar Dangote.
Idan ba a manta ba a watan Disambar 2019 Kodinatan shirin yi wa yara allurar rigakafi a karkashin hukumar WHO Pascal Mkand ya ce Najeriya za ta iya samun shaidar rabuwa da shan inna kwata-kwata idan daga yanzu zuwa karshen shekaran 2020 ba a samu rahoton bullowar cutar a kasar ba.
Mkanda yace hakan zai tabbata ne idan kwamitin ERC ta gamsu da ingancin kokarin kawar da cutar da gwamnatin kasar take yi.
Discussion about this post