Shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya ya bayyana cewa tabbas duk abin da ya samu jam’iyyar APC dole Najeriya ta ji a jika.
A tattaunawa da yayi da manema labarai a fadar shugaban kasa, Sanata Lawan ya ce baya ga tattauna matsalar tsaro da ya addabi musamman jihohin Arewacin Najeriya, ya tattauna da shugaba Muhammadu Buhari game da matsalolin da ke neman dulmiyar da jam’iyyar APC a Najeriya.
” Mun yi tattauna mai zurfi da shugaba Buhari game da tabarbarewar tsaro a kasar nan musamman yankin Arewacin Najeriya. Na shaida masa halin da ake ciki da kiraye-kirayen da wasu ke yi saboda matsin da suka fada a dalilin rashin tsaro.
” A gaskiya lokaci yayi da dole manyan hafsoshin tsarin Najeriya su maida hankali domin kawo karshen wannan matsala. Idan mutum ba zai iya ba, ya sallame shi, shine ya fi dacewa. Ba wai kullum a ce za a gyara amma kuma gyarar ya gagara. Kullum jiya iyau.
Bayan haka Sanata Lawan ya tattauna batun rashin sanin gabanta da jam’iyyar APC ta fada ciki.
” Jam’iyyar APC ke da shugaban kasa, gwamnoni masu yawa, komai na karkashin mulkin jam’iyyar APC a Najeriya, idan ta samu kanta cikin halin rudani, kowa sai ya ji a jikin sa a Najeriya. Dole a dinke barakar da ta dabaibaye jam’iyyar tunda wuri. Hakan duk na daga cikin abubuwan da muka tattauna da shugaba Buhari.
” Ba za mu zuba ido mu bari jam’iyyar na tangal-tangal ba, tana neman ta kife bamu tattataro ta ba. Wannan na daga cikin tattaunawar da nayi da shugaba Buhari. Dole mu san inda muka dosa tun da wuri a dinke barakar da ke neman yagalgala jam’iyyar.
Discussion about this post