Na rungumi Kaddara – Inji Oshiomhole

0

Tsohon shugaba Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana cewa ya rungumi kaddara bisa hukuncin da kwamitin Zartaswar Jam’iyyar ta dauka a makon nan na rushe kwamitin gudanarwar jam’iyyar da yake shugabanta.

” An kira taron kwamitin zartaswar jam’iyyar, kuma a karshe zaman kwamitin an rusa kwamitin gudanarwar jam’iyyar wanda nake shugabanta.

” Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kira ni har ofis ya ce mini ” Idan baka kawo sauye-sauye masu ma’ana a jam’iyyar nan ba, nasara a 2019 zai yi mana wuya.

” Kuma na sani kawo sauyi zai zo da kalubalen sa iri-iri domin sai an dauki wasu matakai masu tsauri da ba zai faranta wa wasu rai ba, amma kuma nawa sai ya zama matsalar gaske, kowa yana adawa da salon taku na. Na amince da hukuncin da suka yanke, ni dai na san na yi iya kokarin dazan iya.

Idan ba a manta ba Kwamitin Zartaswa na Kasa na Jam’iyyar APC, ya nada Gwamna Mai Mala Buni na Yobe a matsayin Shugaban Rikon Kwarya na Jam’iyyar APC na Kasa.

Nada shi ya biyo bayan sauke Kwamitin Gudanarwa na Kasa na APC da aka yi, wanda ke karkashin shugabancin Adams Oshiomhole, wanda kotu ta jaddada dakatar da shi daga jam’iyyar.

An dora wa Buni ci gaba da rikon ragamar APC duk da nauyin rikon jihar Yobe da ke hannun sa.

Buni shi ne Sakataren APC na Kasa har zuwa 2019, lokacin da ya zama gwamnan jihar Yobe.

Mataimakin Sakataren APC na Kasa, Victor Giadom ne ya kira taron wanda shi ne ya yi ikirarin zama Shugaban Riko a lokacin da Babbar Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta jaddada dakatarwar da aka yi wa Adams Oshiomhole daga jam’iyyar APC a mazabar sa cikin Karamar hukumar sa a jihar Edo.

NEC dai shi ne kwamiti na biyu mafi girma a APC, baya ga taron gangamin jam’iyya na kasa.

Sai dai kuma akasarin mambobin Kwamitin Gudanarwa ba su goyi bayan taron ba, wanda Giadom ya kira, sun ce shi ma ba halastaccen mamba din NWC ba ne.

Share.

game da Author