Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya goyi bayan soke takarar Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a karo na biyu.
Da ya ke jawabi ga manema labarai a taron karin bayani dangane da halin da jihar ke ciki kan cutar Coronavirus, Ganduje ya ce Kano za ta yi bakin duk wani kokarin da za ta yi domin ganin jam’iyyar su ta APC ta yi nasara a zaben, wanda za a gudanar cikin watan Satumba, 2020.
Ganduje, wanda ya yi kaurin suna tun bayan harankazamar zaben Kano na ‘inconclusive’, ya ce sun goyi bayan hana Obaseki sake tsayawa takara, saboda APC a cewar sa na tafiya ne bisa wasu ka’idojin da doka ta tanadar.
Don haka ya ce idan aka sake tsaida Obaseki, za a iya fuskantar rasa kujerar, ko da kuwa shi ne ya yi nasara, kamar abin da ya faru a Jihar Bayelsa.
APC ta hana Obaseki sake tsayawa takara sakamakon ruguntsimin rikicin sa da Shugaban APC na Kasa, Godwin Obaseki.
Kwamitin Tantance ‘Yan Takara ya ki tsayar da Obaseki a bisa zargin ya na da matsala da takardun jarabawar sa na jami’a.
Sai dai kuma su na sane da wannan takardun ne amma kuma suka tsayar da shi a 2016 ya ci zabe.
A madadin Obaseki, Oshiomhole ya kinkimo Eze Iyamu, a matsayin Dan takarar APC na zaben gwamnan jihar Edo
Idan ba a manta ba, Oshiomhole ya rika kiran Iyamu mutumin da bai kamata a damka wa amana ba, a lokacin da Iyamu ya ke takarar gwamnan Edo a karkashin PDP, a zaben 2016.
Shi kuwa Gwamnan Kano, Ganduje, tuni har ma ya hango nasara ga APC a zaben.
“Dangane da zaben gwamna a jihar Edo, to Jihar Kano na nan yanzu haka ta na yin duk abin da za ta iya yi, domin APC ta ci zaben gwamnan Edo. Saboda an bi duk wata hanyar da ta dace. Zabe kam, APC ce za mu yi nasara a Edo.” Inji Ganduje.