MU ZUBA MU GANI: Oshiomhole zai dandan radadin karfin kujerar mulki na gwamna da nake kai a zabe mai zuwa – Inji Obaseki

0

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya kalubalanci shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole, cewa ya gama shirin shi tsaf, zai dandana radadin karfin kujerar mulki da yake kai na gwamna mai ci kuma dan takara a zaben gwamna dake tafe.

Obaseki ya maida wa shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole martani cewa kujerar mulki da shi Obaseki yake takama ya na a kai ba za ta yi masa tasiri ba a zaben gwamna mai zuwa.

Ta kicime tsakanin gwamna Obaseki da Oshiomhole da ya kai ga jam’iyyar APC karkashin shugabancin Oshiomhole ta hana Obaseki takara a jam’iyyar.

Hakan ya sa an yi ta kai ruwa rana tsakanin magoya bayan Obaseki da Oshiomhole a jihar..

Obaseki dai shine wanda ya gaji Oshiomhole a jihar bayan ya kammala wa’adin sa na gwamna. Jim kadan bayan darewarsa kujerar gwamna, ya fallo takobin yaki da Oshiomhole.

Bayan korar Obaseki daga APC, gwannan ya garzaya zuwa jihohin Ribas da Akwa-lbom domin ganawa da gwamnonin jihohin.

Ana ganin dai Obaseki zai canja sheka ne daga APC ya koma PDP domin samun damar yin takara.

Obaseki a Aso Rock

A ranar Talata, Obaseki ya ziyarci shugaban Kasa Muhammadi Buhari a fadar Aso Rock.

Bayan ya fito daga ofishin shugaba Buhari, Obaseki ya zanta da manema labarai da suka yi cirkocirko suna jiran sa ya fito su sha labari.

” Na farko dai shugaban jam’iyyar APC Oshiomhole ya ce wai akwai mishkila a takardun karatu na. Abin tambaya a nan shine ta yaya tsantsagwaran dakiki wanda bai yi makaranta ba zai kori wanda yayi makaranta, kuma wai har ya gano bani da takardun kwarai.

” Oshiomhole bai yi makaranta ba, bai san me ake kira takardun makaranta ba da har zai ce wai ni nawa takardun akwai mishkila a ciki.

” Oshiomhole na tsoro da shakkan duk wani da ya sani mai ilimi ne, saboda ya san za a samu ci gaba, ba irin sa ba dake kudundune wuri daya, in bada kitsa banga da tashin hankali babu abin da ya sani.

“Mu zuba mu gani.”

Share.

game da Author