‘Ya’yan jam’iyyar APC da suka dakatar da shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole daga jam’iyyar APC a mazabar sa, sun ce suna nan kan bakan su na korar Oshiomhole da suka yi amma kuma ba za su bi gwamnan jihar ba zuwa jam’iyyar PDP.
Shugaban jam’iyyar APC na Karamar hukumar Etsako West, karamar hukumar da Oshiomhole ya fito, ya shaida cewa suna nan kan bakan su na dakatar da Oshiomhole daga jam’iyyar amma kuma ba za su bi gwamnan jihar Obaseki zuwa jam’iyyar PDP ba.
” Ko a baya ma mun dakatar da Oshiomhole ne saboda rawar da yake takawa wajen tarwatsa jam’iyyar jihar.
Godwin Obaseki ya koma PDP
Jam’iyyar PDP ta daga wa gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya fafata a takarar fidda gwani da da jam’iyyar za ta yi.
A ranar Juma’a ne, gwamna Obaseki ya sanar da canja shekar sa daga jam’iyyar APC zuwa PDP. Hakan ya biyo bayan hana shi takara da jam’iyyar APC ta yi cewa an gano mishkila a takardun sa na karatu.
Kafin ya ambata komawar sa PDP sai da ya yi ganawa ta musamman da shugabannin jam’iyyar PDP da ya hada da yin ziyara ta musamman ga gwamnonin jihohin Ribas Nyesom Wike da Emmanuel Udom na AkwaIbom.
Jam’iyyar PDP ta ce ta jirkita wasu sassa na dokokin ta domin ba gwamna Obaseki dama ya yi takarar fidda gwani da sauran ‘yan takarar jihar a Inuwar jam’iyyar.
Shima tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya yi wa gwamna Obaseki lalale maraba da zuwa jam’iyyar PDP.
Atiku yace wannan kamu da jam’iyyar PDP tayi shirgegen kamu musamman a wannan lokaci da zaben jihar ya tunkaro.
Ya yi kira ga mutanen jiahr Edo da su zabi jam’iyyar PDP a zaben gwamna maizuwa.
Ita kuwa jam’iyyar APC, ta fada cikin tsaka mai wuya tun bayan dakatar da shugabanta Adam Oshiomhole da kotun daukaka kara tayi.
Ana ta kai ruwa rana tsakanin shugabannin jam’iyyar inda daya daga cikin su, Victor Goidam ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar bayan kotu ta dakatar da Oshiomhole.
SHARE.
Discussion about this post