Farawa da Bisimilla, shahararren dan wasan kwallon kafa ta Barcelona da ya fi kowa iya murza tamola a duniya, Leo Messi ya jefa kwallo ta hudu a wasan kungiyar ta farko bayan dawowa daga hutun Korona a kasar Spain.
Barcelona ta yi tattki har zuwa garin Mallorca a matsayin baki amma kuma ‘yan Mallorca basu sha da dali ba.
Wadanda suka jefa kwallo a ragar mallorca sun hada da Bidal, Braithwaith, Alba sai kuma Leo Messi.
Barcelona ta yi canjin ‘yan wasa biyar kamar yadda sabon dokar wasan Laliga ya zayyana saboda yawan wasannin da za a yi a lokaci dan kankani.
Za su buga wasan su na biyu tsakiyan makon gobe.
Real Madrid zata buga wasan ta ranar Lahadi a gida tsakanin ta da eibar.