Gwamnatin Jihar Bauchi ta bada sanarwar cewa Mataimakin Gwamnan Jihar, Baba Tela ya kamu da cutar Coronavirus.
Tela dai shi ne Shugaban Kwamitin Yaki da cutar Coronavirus a Jihar Bauchi.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta hannun kakakin yada labarai na Gwamna Bala Muhammad mai suna Mukhtar Gidado, ya bayyana cewa an yi wa Tela gwaji bayan ya yi korafin kamuwa da wasu alamomi da sagwangwaman da ke da nasaba da cutar Coronavirus.
Sanarwar wadda aka fitar safiyar Laraba, ta ce an bi duk wadanda suke makusantan Mataimakin Gwamna duk an dauki gwajin su, kuma an umarce su duk su killace kan su, kafin fitowar sakamakon gwaji.
“Gwamnatin Jihar Bauchi na sanar da cewa Mataimakin Gwamna Sanata Baba Tela ya kamu da cutar Coronavirus. An yi masa gwaji an tabbatar, kuma tuni ya killace kan sa. Su ma makusantan sa an debi gwajin su kuma an ce su killace kan su.
“Yanzu haka Tela ya killace kan sa, kuma akwai jami’an kula da lafiya masu kula da shi a koda yaushe.”
Gwamna Bala Mohammed ya yi wa Tela fatan samun sauki cikin gaggawa tare da nuna jimamin shigar da ya yi cikin irin halin da gwamna ya fara shiga, na kamuwa da cutar Coronavirus a farkon bayyanar ta a Najeriya.
Ya zuwa 2 Ga Yuni, Coronavirus ta kama mutum 241 a Bauchi, yayin da 221 sun murmure, an sallame su, amma takwas sun mutu.