Sanata Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo, surikin gwamnan jihar Kano ya rasu yana da shekara 70 a duniya.
Sanata Ajimobi ya rasu bayan yayi fama da rashin lafiya mai tsanani a wani asibiti a Legas.
Gwajin cutar da ta yi sanadiyyar rasuwar sa ya nuna Korona ce dsa ta ci rai sama da 500,000 sannan kuma ta miliyoyin mutane sun kamu da ita.
fitaccen dan siyasa ne kuma gawurtaccen mai kishin kasa. Dan sa ya auri ‘yar gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a shekarar bara.
Shine gwamnan jihar Oyo na farko da ya yi nasarar ta zarce a siyasar jihar.
Allah ya ji kansa, Amin.
Discussion about this post