Makiyayan Jihar Kano sun koka kan yadda wata cuta ke wa shanun su kisan-farat-daya

0

Wata cuta mai yi wa shanu kisan-farat-daya ta bayyana a jihar Kano, inda a yanzu haka ta ke ci gaba da kashe shanu masu dimbin yawa a garake da rugage cikin jihar.

Shugaban Kungiyar Masu Kiwon Shanu da Madara ta Jihar Kano, Usman Abdullahi ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES.

Abdullahi ya ce a Turance dai ana kiran cutar ‘Contagious Bovina Pleuropneumonia’, wato CBPP.

Yadda cutar ke farawa a cikin saniya ko sa, da farko ta na fara kama huhu, sai zazzabi daga nan kuma sai saniya ta kasa yin numfashi kamar yadda ta saba. Sai kuma tari da yawan dalalar majina ta hanci.

Cutar wadda ya ce ta fi kama shanu da dorinar ruwa, ta fara bulla ne a Najeriya tun cikin 1924. Ya zuwa 1960 ta sake bulla kusan sau 200 a wurare daban-daban a Barno da Kano.

An dakile ta cikin 1965, amma ta sake bulla daga bisani.

A yanzu Abdullahi ya ce sama da shanu 100 cutar ta kashe a wasu rugage da ke karkashin Karamar Hukumar Bunkure a Jihar Kano.

Premium Times ta tattauna da wani wanda ya rasa shanu 50, mai suna Muhammadu Babiye.

Shi kuwa Abdullahi, ya yi korafin cewa jami’an Ma’aikatar Noma da Jami’an kula da cutar dabbobi, duk sun san halin da ake ciki, an kai musu rahoton bayyanar cutar, amma ba su yi komai ba.

“Mu na kira a bai wa makiyayan nan diyyar shanun da aka rasa, domin jama’a su rage damuwa.”

A karshe ya yi kira da a yi musu abin da ya dace tun tuni a yi musu, wato alluran riga-kafi ga shanun.

Ya ce amma dai ba zai manta ba jami’an kuda da dabbobi sun bi daga baya suna duba shanu su n kuma ba su magani.

Ya yi kiran da a sa jami’ai su rika zagayawa akai-akai su na lura da irin halin da dabbobin jama’a ke ciki.

Hakan inji shi zai rage yawan asarar dabbobi da makiyaya da manoma ke yi.

Share.

game da Author