Basaraken Iwu, Abdulrosheed Akanbi, ya bayyana cewa zai raba wa matan dake karkashin masarautar sa tankadadden barkonon da za su rika fesa wa kwarto aduk lokacin da ya tunkare su.
Basaraken ya kara da cewa yayi haka ne a matsayin gudunmawar da zai ba al’ummar sa domin rage yawa-yawan fyade da ake samu a tsakanin al’umma a yanzu.
Za a raba wannan barkonon fesawa ranar litinin 15 ga Yuni.
” Ana gayyatar mata dake yankin Iwo, Ayedire da Ola Oluwa da su garzayo fadar sarki Akanbi da karfe 10 na safe domin karbar wannan barkono. An so a zo da wuri domin akwai yar gajeruwar ganawa da zai yi da su da kuma koya musu yadda za su yi amfani da shi.
Fyade ya zama ruwan dare a Najeriya. Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta kawo muku labaran yadda ake yi wa yara mata kanana fyade da tsofafaffi.
Haka kuma PREMIUM TIMES ta kawo muku labarin wani tantirin mai yi wa yara da tsoffi fyade da dubun sa ya cika a Kano.
An damke Alfa wanda aka fi sani da lakabin ‘Mai Skirt’, a lokacin da ya shiga wani gida tsakar dare da nufin yi wa wasu kananan yara fyade.
“Ya shiga dakin su sai ya kashe fitila. Yayin da mahaifiyar yara ta lura an kashe fitilar dakin, sai ya yi sauri ta tashi mijin ta daga barci. Shi kuma ya kwartsa ihu, kwarton ya gudu. Amma aka fafare shi aka damke shi.”