Majalisar Tarayya ta ki yarda a kafa dokar dandake wanda ya yi fyade

0

Majalisar Tarayya ta amince a Yankee wa mai laifin fyade tsatstsauran hukunci, amma ba ta amince a kafa dokar dattake duk wanda ya yi fyaden ba.

An dai shafe kusan awa biyu ana yamutsa gashin baki a majalisa kan batun fyade da ya zama ruwan dare yanzu a fadin kasar nan.

Hayaniya ta kaure yayin da Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya nemi sanin wane irin hukunci ne ya dace a yi wa mace gyarumar da ta yi wa yaro fyade.

A karshe dai Majalisar Tarayya ta nemi a tsaurara hukunci a kan masu fyade, kamar yadda ita ma Majalisar Dattawa ta amince a ranar Talata.

Mambobin sun yanke cewa rashin kwakkwaran hukunci, talauci da kuma wasu gurbattaun dabi’u da al’adu ne ke kara haifar da yawaitar fyade a cikin al’umma.

Kakaf din mambobin sun amince za su sako bakaken kaya zuwa zauren majalisa a ranar Talata Mai zuwa, domin nuna jimami ga wadanda aka yi wa fyade a kasar nan.

Idan ba a manta ba, Kama wasu mutum 11 da suka you wa yarinya ‘yar shekara 12 fyade a Jigawa, ya haifar da bacin rai sosai a Arewacin kasar nan da ma kasa baki daya.

Haka nan kuma yi wa wata yarinya ‘yar shekara 23 fyade a cikin coci a Jihar Edo, sannan aka kashe ta, ya haifar da matukar bacin rai a kudanci da kasar nan baki daya.

Yarinyar mai suna Vera Omozuwa, daliba ce a Jami’ar Benin da ke ajin ta na farko.

Share.

game da Author