Majalisar Dattawa ta aika wa Babban Bankin Najeriya (CBN) kakkausar wasikar neman yadda aka yi dala bilyan 3.3 suka salwanta a cikin asusun Babban Bankin Tarayya, CBN.
Makudan kudaden dai daidai suke da naira tiriliyan 1.2 na kudin Najeriya.
Sannan Kuma wadannan kudade da aka nema aka rasa, su na daga cikin dala bilyan 21.3 da Hukumar Tara Kudaden Shiga (FIRS) ta tara a harajin hada-hadar kasashen ketare, cikin 2015.
FIRS ta damka kudaden ajiya a CBN, kuma ta aike wa Akanta Janar na Tarayya adadin kudaden a kididdige.
Sai dai kuma a rubuce shi kuma CBN ya rattaba cewa kudaden yanzu dala bilyan 18 ne kacal.
Mataimakin Gwamnan Babban Banki, Edward Adamu, ya shaida wa Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Lura da yadda ake kashe kudaden Gwamnatin Tarayya cewa, e tabbas da farko kudaden dala bilyan 21.3 din ne FIRS ta kai CBN.
To amma a yanzu kudaden sun zaizaye sun koma dala bilyan 18 saboda yawan faduwar-‘yan-bori da naira ke yi yi da kuma yadda ita kan ta dala din wani lokaci ta ke yin tashin kumfar gishirin Andurus.
Tun farko dai Ofishin Akanta Janar ne ya aika wa Majalisar Dattawa wannan korafi, ita kuma Majalisa ta aika wa CBN.
Shugaban Kwamitin Lura da Kashe Kudaden Gwamnati, Sanata Mathew Urhoghide, dan PDP daga Jihar Edo, ya ce Bai gamsu da bayanin yadda kudaden suka zaizaye ba.
Saboda haka ya ce CBN ya sake bayyana a gaban Kwamitin mako mai zuwa.
“Akwai wasikun tambayoyin salwantar kudade har guda 13 da muka aika wa CBN. Amma har yau babban bankin ya kasa yin bayanai a kan wasu. Cikin wadanda ya kasa you bayanan kuwa har da wadannan dala bilyan 3.3 da suka you fukafuki ko suka zaizaye.” Inji Sanata Mathew.