Akalla mutum 21 ne mahara suka kashe a kananan hukumomin Talata Mafara da Maru a jihar Zamfara.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce mutum 21 aka kashe sai dai mazaunan wadannan kananan hukumomi sun shaida cewa maharan da suka diran musus a ranakun Talata da Laraba sun kashe mutum 25 ne.
Wani mazaunin kauyen da baya so a fadi sunan sa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun fara diran wa karamar hukumar Talatan Mafara ne, inda suka kashe mutane da dama sannan suka sace dabbobi masu yawa.
Ya kuma ce mahara sun yi bata kashi da yan banga a wasu kauyukan da suka afka.
Bayan haka ne suka sake dawowa washe gari ranar Laraba inda suka afka wa kauyukan Awala Zaman Gida, Yargada Bolakke, da Gidan Runji dake kananan hukumomin Maru da Talata Mafara.
Maharan sun kuma kasashe mutane a makabarta yayin da suke jana’izan ‘yan uwansu da maharan suka kashe a harin farko.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Muhammad Shehu ya tabbatar da kai wannan hari inda ya ce mahara sun far wa kauyukan Tungar Malan, Manyan Karaje, Tungar Arne, Dangodon Maiyakane, Dangodon Mai Masallaci da Boleke a karamar hukumar Maru.
Ya ce maharan sun far wa kauyukan ne domin su sace dabobbi amma suka yi bata kashi da ‘yan banga wanda aka fi sani da ‘YAN SAKAI.
A dalilin haka mutum 15 sun mutu sannan 7 sun ji rauni.
Shehu ya ce a ranar 3 ga watan Yuni maharan sun far wa kauyuka hudu da suka hada da Gidan Dan Kani, Tungar lauti, Inwala and Dangodo dake karamar hukumar Talata Mafara.
Ya ce mahara sun kuma far wa mutanen dake jana’izan ‘yan uwansu da maharan suka kashe a harin da suka kai a ranar farko.
A sanadiyyar haka mutum biyar sun samu rauni a jikinsu kuma an kai su asibiti ana duba su.
A karshe ya ce jami’ai za su bi sahun wadannan ‘yan ta’adda domin ragargaza su.
Discussion about this post