Masu Garkuwa da mutane da suka sace wani likita dake aiki a Abuja mai suna Benedict Audu mai shekaru 70 tare da dansa da abokin sa sun kashe su bayan sun karbi naira miliyan 70 kudin fansa.
Benedict da dan sa tare da abokin sa na hanyarsu na zuwa garin Katsina Ala ne daga Takum dake jihar Taraba inda masu garkuwa suka sace su.
An yi ta kai ruwa rana tsakanin iyalan wadanda aka sace da masu garkuwan kan kudin fansa inda daga karshe aka biya naira miliyan 7 kudin fansa.
An gano cewa likita Benedict sai da ya biya su naira 500,000 ta banki a inda suke tsare da shi. Bayan sun sun karbi kudaden duka sai suka kashe su su ukun suka rufe su a wani rami.
Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta bayyana cewa ta kama wasu matasa biyu da ake zargin su da hannau a sace likita da dansa.
‘Yan sandan na ci gaba da bincike domin gano sauran wadanda ke da hannu a aikata wannan mummunar abu.