Kakakin kungiyar Gwamnonin Najeriya Abdulrazaque Bakindo, ya bayyana cewa kalaman da aka ruwaito wai sun fito daga bakin gwamnan jihar Ribas ne ba haka bane.
Barkindo ya ce wannan Kalamai daka bakin kwamishinan sa ne ba gwamnan jihar ba.
” Gwamna Wike cikakken dan kungiyar ne kuma a duk lokacin da kungiyar ke ganawa ya kan turo mataimakiyar sa ta wakilce sa. Ba zai furta irin wadannan kalamai ba, ” yan Maula…” Kwamishinan sa ne ya fadi haka amma ba Wike.
” Sannan kuma akwai banbanci tsakanin kungiyar gwamnonin Najeriya da kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki, shi bai sani ba. Sai ya gwarmatsa komai wuri daya. Wike ba zai fadi haka ba kamar yadda ya rubuta.
Idan ba a manta ba gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya kira gungun Kungiyar Gwamnonin Najeriya 35 cewa taron yuyuyu ne, daga mabarata, ‘yan maula sai wadanda ba su san ciwon kan su ba.
Wannan fatattaka da ya yi musu, ta biyo bayan kasa yin wani katabus da ya ce sun yi, wajen ganin sun hana a soke takarar Gwamna Obaseki na Jihar Edo, dan APC.
Wike, wanda dan PDP ne, ya ce Kungiyar Gwamnonin Najeriya ba ta da wani amfani, domin ta na ji ta na gani dan kungiyar sa zai shiga matsala, amma ba za ta iya taimakon sa ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka ki tantance Obaseki bisa zargin ba shi da kyakkyasan takardun kammala karatun sa.
Ranar Litinin Obaseki ya ziyarci Wike da Udom Emmanuel na Cross Rivers, a kan hanyar sa ta komawa jam’iyyar PDP, domin ya nemi takara a can.
“Kafin zaben 2015, Kungiyar Gwamnonin Najeriya na da karfi fiye da kima. Amma jam’iyyar APC ta kashe kungiyar. Saboda Shugaban Kungiyar Gwamnan APC.
“Wai mutumin da ba shi da wasu takardun karatu, shi ne zai shiga gaba su hana Obaseki takara bisa zargin takardu. To shi ina na sa.
“Me ya sa Oshiomhole bai nemi gafara ga ‘yan Najeriya ba, saboda a 2016 shi ya tsaida musu Obasekin da ya ce a yanzu ba shi da cikakkun takardun tsayawa takara!
“A zaben 2019 na samu matsala, Gwamnatin Tarayya ta janye dukkan jami’an tsaron da ke tare da ni, yadda suka bar ni a cikin babbar barazana.
“Na kira Kungiyar Gwamnonin Najeriya na sanar da su halin da na ke ciki. Amma da ya ke NGF din majen Lami ce, ba cizo ba yakushi, ba ta yi mini na kokari.
“Mu dubi gwamnonin APC masu kiran kan su wai ‘Yan Neman Ci Gaba. Su na gani aka wulakanta dan uwan su Obaseki dan APC. Amma sun yi tsaye sototo, ba su yi komai ba.
Ministan Yada Labaran Wike, mai suna Paulinus Nsirin ne ya fitar da jawabin Gwamna Wike.
Wike ya ce Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro da INEC sun yi masa taron-dangi a lokacin zaben 2019, amma duk ya watsar da su, Allah ya kunyata su.
Ya ce ya na fatan al’ummar jihar Edo ba za ta amince a yi mata karfa-karfa ba.