Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Arewa da su toshe kunnuwar su kan korafin da kungiyar dattawan Arewa karkashin Kodinatan ta Farfesa Ango Abdullahi cewa wai bata tabuka komai ba game da tsaro.
Idan ba a manta ba Kodinatan kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa yanzu fa tura ta kai bango kan matsalar tsaro a Arewa domin mutanen yankin na shan azabar mahara da ‘yan bindiga.
Abdullahi ya ce, in banda cika baki da gwamnatin Buhari ke yi, sannan a kullum ana kashe mutane kamar kaji a yankin babu wani nasara da take samu.
A martani da fadar ta maida wa kungiyar, ta hannun mai bada shugaba Buhari shawara kan harkar yada labarai, Femi Adesina, fadar tace farfesa Ango ba da yawun ‘yan Arewa yake magana ba, ” Mutum ne wanda duk ya gaji ma sannan kamar ma ya rude. Bamu canja daga matsayin da muka saka wannan kungiya ta sa ba.
” Idan kuka ji irin wannan sanarwa ya fito daga kungiya mai suna ‘Kungiyar Dattawan Arewa, NEF, za ku dauka da gaske dattawan Arewa ne, amma ku sani ba su bane fa. Kungiyar NEF ta Ango Abdullahi ce shi kadai tilo, babu wani da ke tare da shi cikin Dattawan Arewa, shi kadai yake aman sa ya lashe.
“Kafin 2019, Ango Abdullahi da rundunar sa shi-shi kadai ya nuna kiyayyar sa karara ga shugaba Buhari kuma ya nuna dan takarar da yake so, amma da shi da dan takarar na sa sun sha kayi a hannun ‘yan Najeriya.
” Kungiyar NEF ta na ta rangaji ta tangaririya kamar wadda ke jiran mala’ikan mutuwa. Shugaba Buhari na kokarin canja fasalin kasar nan zuwa turba nagari , sannan baya boye wa ‘yan Najeriya halin da kasa ke ciki. Basu bukatar wani yayi azarbabi ko kadifirin ga ya musu halin da kasa ke ciki.
Karanta labarin mu na baya:
Kodinatan kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa yanzu fa tura ta kai bango kan matsalar tsaro a Arewa domin mutanen yankin na shan azabar mahara da ‘yan bindiga.
Abdullahi ya ce, in banda cika baki da gwamnatin Buhari ke yi, sannan a kullum ana kashe mutane kamar kaji a yankin babu wani nasara da take samu.
Ya ce mutane sun gaji da cika bakin gwamnatin Buhari.
” Yadda mahara da ‘Yan bindiga suke cin karen su ba babbaka a yankin Arewa yanzu ya sa mutane ba su da karfin yin komai sai yadda suka yi da su. Su afka wa kauye su kashe da kashewa, su sace na sacewa sannan su yi tafiyar su lafiya lau, gobe sai a fito a ce ana gama da su, a ina a ka gama da su?
” Karara dai ya nuna gwamnatin Muhammad Buhari da gwamnoni musamman na yankin Arewa fa abin ya fi karfin su. Ba za su iya tabbatar da tsaro a yankin Arewa ba, wanda shine hakkin da ya rataya a kan su.
” Abin yanzu yayi tsanani matuka domin su kan su maharan sun gane akwai wawukeken gibi a harkar tsaro a kasar nan da ya sa sukan yi abinda suka ga dama babu waiwayen baya. A matsayin mu na dattawan Arewa muna tare da miliyoyin yan Najeriya dake kwana addu’a Allah ya kawo mana karshen wannan matsala na tsaro a Kasar nan sannan da rokon mahukunta da hakkin haka ya rataya a kansu su samar wa mutane tsaro kamar yadda suka yi alkawari.
” Lokaci yayi da dole mu fito muce wahalar ya isa haka. An san mutanen mu da bin doka da oda. Amma ya kamata gwamnati ta sani tura ya kai bango yanzu. Akwai yiwuwar a fita a yi gangami na zanga-zanga wanda doka ta basu damar haka domin jawo hankalin shugaba Muhammadu Buhari da mahukunta su saurari kukan mutane.
” Matsalar da muka shiga a Arewa ya tabbatar mana da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaza, ba za ta iya ba, wannan shine gaskiyar magana. Ba za mu yarda da haka ba. Gwamnati ta inganta tsaro a yankin Arewa shine damuwar mu. Mun gaji da cika baki, Kullum ace an gama da su ko kuma an yi nasara bayan karara, kowa na gani an gaza, abu dai ya fi karfin mahukuntar wannan gwamnati.
Discussion about this post