Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar amincewa da fara zirga-zirgar jigilar jiragen haya a fadin kasar nan, a bisa sharuddan yin kaffa-kaffa da kiyayewa daga kamuwa da cutar Coronavirus.
A ranar Litinin ce Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Yaki da Cutar Coronavirus, Boss Mustapha ya bayyana haka.
Ya ce sai dai ya na sanar da cewa kowa ya yi shirin shiga jirgin sama da sanin cewa farashin tikiti zai kara tsadar gaske.
Ya ce wannan tsada da za a fuskanta ta samu ne sanadiyyar karuwar farashin kayayyaki a bangaren sufurin jiragen sama, tun bayan barkewar cutar Coronavirus.
“Ko a cikin kasuwanni farashin kayayyaki sun kara tashi sosai. To hakan ya shafi bangaren sufurin jiragen sama. Musamman ina wasu ka’idoji da aka bijiro da su a dalilin cutar Coronavirus, sun sa tilas za a sha tsadar tikitin jiragen sama.”
Najeriya ta rufe filayen jiragen ta cikin watan Maris bayan barkewar cutar Coronavirus a kasar nan, wadda a yanzu ta ci rayuka sama da 500.
A Amurka cutar ta kashe mutum sama da 125,000.
Ranar 21 Ga Yuni ce aka ce za a fara bude wasu filaye biyar a kasar nan.
Sai dai kuma kamfanonin sufurin jiragen sama sun ce ba su kammala shirye-shiryen da suka wajaba su kammala ba, kafin jiragen su su fara lodin jigilar fasinjoji.
A ranar Asabar ce Ma’aikatar Sufurin Jirage ta yi duba-garin irin shirin da aka rigaya aka kammala da kuma yin gwajin lafiyar wasu na’urori.
Karin Kudi
Daga cikin karin kudin da za a fuskanta har da karin kudin ‘Sauka-lafiya’, wanda kowane fasinja ke biya idan ya sauka filin jirgi.
Za a kara harajin daga naira 1,000 zuwa naira 2,000.
Sannan kuma za a hana jirage yin ‘ful-lodi’, domin kiyayewa da dokar ka’idar hana gwamutsuwar jama’a a kusa-da-kusa.
“Wato jirgin da ke daukar mutum 150, a yanzu sai dai ya dauki fasinja 100 ko 75 kadai a tashin lodi daya.
Discussion about this post