Kotun ECOWAS ta umarci gwamnatin Najeriya ta biya sojoji 244 da aka kora dukkan hakkokin su

0

Kotun Sauraren Kararraki ta Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) da ke Abuja, ta umarci Gwamnatin Najeriya ta gaggauta biyan hakkokin da suka hada albashi da sauran kudaden da sojoji 244 da aka sallama cikin 2016 ke bin gwamnati.

An dai kori sojojin su 244 cikin 2016, bayan an same su da laifin tserewa yayin da suke gumurzun fada da Boko Haram.

Korarrun sojojin dai sun ce sun tsere ne saboda an ki ba su isassun makaman da za su iya tunkarar Boko Haram da su.

Bayan an kori sojojin ne sai suka tunkari kotun ECOWAS suka shigar da karar neman gwamnatin Najeriya ta biya su dukkan hakkokin ta da su ka hada da albashi da sauran ariyas na hakkokin kudaden da su ke bin gwamnati.

A hukuncin da Kotun ECOWAS ta yanke ranar 15 Ga Mayu, ta ce gwamnatin Najeriya ta tafka babban kuskuren korar sonojin daga aikin su.

Hukuncin karshe da kotun ta yanke a ranar Alhamis da ta gabata kuma, sai ta umarci gwamnatin Najeriya ta gaggauta biyan sojojin dukkan hakkokin su har zuwa na watan Janairu, 2016.

Babban Mai Shari’a Keikura Bangura, wanda ya ke bayyana hukuncin da ya yanke ta hannun mai yi masa tafinta, ya ce kotu ta yanke hukunci bayan ta saurari korafin da korarrun sojojin 244 suka gabatar a gaban ta. Sannan kuma ta saurari ba’asin gwamnati.

Ya ce hukuncin da yanke a ranar Alhamis din nan, ya shafe wanda aka yanke a shekarar da ta gabata, a ranar 15 Ga Mayu, 2029.

Duk da cewa kotun ba ta ce a maida sojojin su 244 bakin aikin su ba, ta ce korar da aka yi musu ta kauce daga dokar da ta ba su ‘yanci, ciki har da ‘yancin sauraren ba’asin su dangane da dalilin su na tserewa daga wurin yaki.

Sojojin dai sun sake shigar da kara ce a ranar 14 Ga Yuni, 2019, cewa tunda kotu ta ce korar su haramtacciya ce, to a gaggauta maida kowanen su a bakin aikin sa, kuma a matsayin da kowanen su ya ke a aikin soja kafin a kore shi. Sun nemi kuma a biya su dukkan hakkokin su.

Sun kuma nemi a biya su dukkan albashin su na shekarar 2015 gaba dayansu, har ma zuwa lokacin da kotu ta tilasta bin wannan umarni.

Sauran mambobin kotun da suka taya Bangura yanke wannan hukunci, sun hada da Gberi-Be Ouattara da Dupe Atoki.

Share.

game da Author