Kotu ta umarci ‘yan sanda su biya naira milyan 15, diyyar rayukan ‘yan Shi’a uku da suka kashe

0

Babban Mai Shari’a Taiwo Taiwo Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya umarci Rundunar ‘Yan Sanda Najeriya ta gaggauta biyan diyyar naira milyan 15 ga iyalan wasu ‘yan Shi’a su uku da ‘yan sanda suka bindige.

‘Yan sanda sun bindige su ne a ranar 22 Ga Yuli, 2019 yayin da suke zanga-zangar lumana a Sakateriyar Gwamnatin Tarayya, Abuja.

Alkali Taiwo Taiwo ya yanke hukuncin cewa zanga-zangar lumana ce suke yi, babu mai makami dauke a cikin su.

Ya ce tilas ‘yan sanda su biya uku daga cikin su diyyar naira milyan 5 kowanen su.

Za a biya kudaden ga iyalan mamatan wadanda gawarwakin su ukun ke Babban Asibitin Tarayya, Abuja ajiye a dakin ajiye gawarwaki.

Wadanda ‘yan sandan suka bindige har lahira, sun hada da Sulaiman Shehu, Mahdi Musa, Abubakar Faska da Askari Hassan.

Masu shigar da kara sun kuma nemi alkali ya tilasta wa ‘yan sanda buga sanarwar neman afuwar kisan da suka yi.

Sai dai kuma Taiwo Taiwo bai bayar da wannan umarnin ba kamar yadda iyalan ‘yan Shi’ar suka nema.

Iyalan ‘yan Shi’ar da suka shigar da kara akan mamatan sun hada da Ibrahim Abdullahi, Ahmad Musa, Yusuf Faska da Said Haruna.

PREMIUM TIMES ta fahimci cewa tsawon lokacin tun daga shigar da kara har ranar yanke hukunci a yau Litinin, Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ba ta shigar da takardar bayanin jayayya da karar ba, kuma ba ta tura lauya ba.

Share.

game da Author