KORONA: Tattalin arzikin Najeriya zai yi durkushewar da bai taba irin ta ba tun cikin 1980s – Bankin Duniya

0

Bankin Duniya (World Bank) ya bayyana cewa Najeriya za ta afka cikin halin kuncin tattalin arziki, irin wanda rabon ta da afkawa ciki, tun cikin shekarun 1980s.

Bankin Duniya ya ce masifar cutar Coronavirus da kuma mummunan faduwar farashin danyen man fetur ne zai jefa kasar nan cikin mummunan kuncin da milyoyin ‘yan Najeriya ba su taba fuskantar irin sa ba, tun bayan kuncin rayuwar da suka dandana a cikin shekarun 1980s.

A ranar Alhamis din nan ce Bankin Duniya ya fitar da wannan rahoto a Abuja, a cikin bayanan sa na Halin Da Najeriya Ke Ciki, wanda mahukuntan bankin kan buga a kai a kai.

Bankin ya yi wannan kirdadon shiga cikin wannan halin tasku ne idan ma har an dakile Coronavirus tsakanin watannin Yuli zuwa Satumba.

Amma idan cutar ta ci gaba da yaduwa da fantsama fiye da nan da Satumba, to kuncin karyewar tattalin arzikin zai zarce kirdadon da Bankin Duniya din ya yi.

Rahoton ya ce kafin bayyanar Coronavirus, an yi hasashen tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa da kashi 2.1 kacal a cikin shekarar 2020.

A yanzu kuwa Bankin na Duniya ya ce ko ma a yanzu aka dakile Coronavirus, to cutar da kuma faduwar farashin gangar danyen man fetur a duniya ya karya lagon tattalin arzikin Najeriya.

A kan haka ne ya ce akalla mutane milyan 5 za su kara talaucewa su koma fakirai a Najeriya, cikin 2020.

Masu kananan hada-hadar kasuwanci za su kara jin jiki sosai, kuma dama kashi 80 bisa 100 na abin da Najeriya ke sayarwa a waje, duk danyen man fetur ne.

“Kashi 30 bisa 100 na harkokin bankunan Najeriya duk harkokin danyen man fetur ne. Kuma kashi 50 bisa 100 na kudaden shigar Najeriya ke takama da su, duk na danyen man fetur ne.”

“Faduwar darajar danyen man fetur da Najeriya ke takama da shi da kuma rashin samun kudaden haraji sakamakon tsaida hada-hada lokacin Coronavirus, ya sa kudaden shigar bunkasar tattalin arziki za su kara yi wa gwamnati kasa, daga kashi 8 a shekarar 2019, zuwa kashi 5 a 2020.

“Fargaba da rashin tabbas din makomar harkoki lokaci da bayan Coronavirus zai sa jarin dimbin jama’a ya ruguje, kanana da manyan ‘yan kasuwa su karye.

“Jama’a za su tsuke bakin aljihun kudaden da suke kashewa a hidimar gida, wadanda idan da za a tattara jimillar su wuri daya, sun haura yawan wadanda aka zuba jarin su a kasar daga baki ‘yan kasashen waje.” Inji rahoton.

Daraktan Bankin Duniya a Najeriya Shubham Chaudhuri ya ce ‘yan Najeriya za su kara shiga mummunan hali na gaba, daga talauci zuwa fakiranci, yayin da ba a san tsawon lokacin da tsare-tsaren inganta tattalin arzikin da gwamnati ta bijiro su za su kai gaci ba.

Ya ce akalla ‘yan Najeriya milyan biyar za su kara talaucewa a cikin shekarar 2020.

“Kashi 49 bisa 100 na masu aiki a wuraren da ba harkokin noma ba, sun ce sanadiyyar Coronavirus ba a biya su albashin watannin Afrilu da Mayu ba.

Share.

game da Author