KORONA: Oyo za ta bude makarantu duk da gargadin ma’aikatar Lafiya ta Kasa

0

Gwamnatin jihar Oyo karkashin gwamna Seyi Makinde ta ci gaba da shirin bude makarantun boko a jihar duk da gargadin kada ta yi haka da gwamnatin tarayya ta yi mata.

Kwamitin yaki da cutar Covid-19 na jihar ta ce gwamnati za ta bude makarantun ne domin dalibai dake aji 6 na firamare, ajin karshe na karamar sakandare JSS 3 da na karshe na babban sakandare SSS 3 su fara karatu.

Sai dai kuma gwamnatin jihar ta ce za a saka wasu tsauraran matakai da dole za a rika bi domin kauce wa kamuwa da Korona.

Duk da haka ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba ya gargaddi gwamnatin da ta hakura da bude makarantu da wa bude makarantu cewa yin haka bai kamata ba.

Matakan da makarantu da dalibai za su bi

1. Malaman makarantun za su dawo aiki daga ranar 29 ga watan Yuni, su kuma dalibai d za su fara karatu daga ranar 6 ga watan Yuli 2020.

2. Gwamnati ta horas da shugabannin makarantu 372 yadda za su kiyaye kan su da malaman su da dalibai a lokacin da suka dawo aiki.

3. Dalibai za su rika saka takunkumin fuska hukumar makarantun kuma za su wadata wuraren wanke hannaye da ruwa da sabulu na dalibai da malamai.

4. Daga ranar 15 ga watan Yuli gwamnati za ta sake duba yadda komai ke tafiya domin dawo da dalibai gaba daya.

5. An yi wa mutum 8,000 gwajin cutar a jihar kuma za a a ci gaba da gwajin cutar a asibitoci.

Sakataren yada labaran gwamna Seyi Makinde Taiwo Adisa ya fitar da wannan hukunci da gwamnati ta yanke.

Share.

game da Author