KORONA: Oyo ta umarci ma’aikata su koma aiki, makarantu su bude

0

Gwamnatin jihar Oyo ta sassauta dokar hana walwala da ta saka don dakile yaduwar cutar coronavirus a jihar.

Gwamnati ta ce daga ranar 29 Yuni duk ma’aikatan gwamnati su dawo aiki.

” Sannan kuma yaran makaranta daga aji 6, JSS 3, SS 3 su dawo domin ci gaba da karatu.”

Maitaimaka wa gwamna Seyi Makinde kan harkokin yadda labarai Taiwo Adisa ya sanar da haka a takarda da ya raba wa manema labarai ranar Litini. Sannan muatne za su ci gaba da walwala tun daga karfe 4 na asuba zuwa 10 na dare.

Ya kuma ce wuraren ibada a jihar za su ci gaba da ibada kamar yadda aka saba a da sai dai kuma za a bi ka’idojin da gwamnati ta saka na kariya daga kamuwa da Korona.

Idan ba a manta ba gwamnati jihar amince wa ma’aikatar daga mataki 13 zuwa sama su fara zuwa aiki tun a ranar 27 ga watan Afrilu amma yanzu gwamnati ta bude duk ofisoshi domin duk ma’aikata su dawo kan aikinsu ranar Litini 22 ga watan Yuni.

“Duk daliban da gwamnati ta amince su fara karatu Za su saka takunkumin fuska, wanke hannaye da amfani da man tsaftace hannaye.

Share.

game da Author