Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO dake Brazzaville kasar Kongo ta bayyana cewa mutum sama da 380,000 ne suka kamu da cutar Covid-19 a Nahiyar Afrika.
WHO ta Sanar da haka ne a shafin ta na twitter dake yanar gizo ‘@WHOAFRO’ ranar Litini.
Bisa ga alkaluman da Kungiyar ta fitar sun nuna cewa mutum sama da 181,000 sun warke kuma 9,500 sun rasu.
Kasashen Afrika ta Kudu,Ghana na daga cikin kasashen Afrika da cutar ta yi wa kamu mai tsanani.
Mutum 138,134 Sun kamu a kasar Afrika ta Kudu sannan 2,456 sun mutu.
A Najeriya mutum 24, 567 sun kamu, mutum 567 sun mutu.
A kasar Ghana mutum 17, 351 sun kamu, 112 sun mutu.
Bayan haka kasashen Lesotho, Gambia da Seychelles ne kasashen da suka fi samun mafi karancin yawan mutanen da suka kamu da cutar.
Kasar Lesotho mutum 27 suka kamu da kwayoyy cutar, mutum 45 sun kamu a kasar Gambia sannan mutum 77 ukan kamu a kasar Seychelles.