KORONA: Mutum 350 sun warke, 19 sun warke a jihar Gombe

0

Kwamitin dakile yaduwar cutar covid-19 dake jihar Gombe ta bayyana cewa an sallami mutum 350 da suka kamu da cutar covid-19 sannan wasu mutum 19 sun mutu a jihar.

Shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar Idris Mohammed ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata a garin Gombe.

Mohammed ya ce a yanzu haka mutum 134 na kwance a wuraren da aka killace su a jihar.

Ya kuma ce ma’aikatan kiwon lafiya na ci gabaa da yin bincike domin gano mutanen da ka iya kamuwa da cutar a dalilin cudanya da mutanen da suka kamu da ita.

Bayan haka Mohammed ya ce babban matsalar da kwamitin ke fama da shine rashin samun adireshin mutanen da sakamakon gwajin cutar ya nuna sun kamu da cutar.

Ya ce hakan na yi wa ma’aikatan lafiya wahalan gano su domin a killace su.

Mohammed ya yi Kira ga mutanen jihar da su hada hannu da kwamitin dakile yaduwar cutar da ma’aikatan kiwon lafiya domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Ya jinjina kokarin da masu ruwa da tsaki suka yi wajen wayar wa mutanen kai game da cutar.

Yanzu dai gwamnati ta kara Ware wasu kudade domin inganta aiyukan kwamitin dakile yaduwar cutar a jihar.

Mutum 503 sun kamu,134 na kwance a wuraren killace wadanda suka kamu da cutar a jihar.

A Najery kuma, mutum 25,133 suka kamu da cutar, mutum 9402 sun warke, 573 sun mutu.

Share.

game da Author