A daidai kasashe na ci gaba da sassauta dokar hana walwala sannan ana bude iyakoki da kasuwanni, ita ma Korona na ci gaba da yaduwa kamar wutan daji.
Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce a karon farko an samu mutum 183,000 d saka kamu da kwayoyin cutar cikin awa 24, wato kwana daya.
Wannan adadi shine mafi yawa da aka taba samu tun bullowar cutar Korona a duniya.
Shugaban hukumar, Tedros Ghebreyesus ya ce alkaluman wadanda suka kamu yana hauhawa ne saboda ci gaba da gwaji da ake da kuma yaduwar cutar da bude wuraren sana’a da kasuwanci da ma’aikatu da gwamnatoci ke yi.
Ya hori mutane da su bi dokokin kiyaye kai daga kamuwa da annobar da suka hada da wanke hannaye, saka takunkumin fuska, bada tazara a tsakanin juna da dai sauran su.
Darekta a hukumar, Michael Ryan ya shaida cewa ba dawowa ne cutar take yi a kasashen da suka jigata da ita ba, ana samun karin mutane ne saboda kasashe masu yawan jama’a a yankin kudancin Amurka da can kasashen Koriya ta Kudu sai yanzu ne cutar take ganiyar ta a can.
” Yanzu ne cutar ta bayyaana a wasu kasashe masu yawan jama’a. Saboda haka dole a rika samun alkaluman wadanda suka kamu na cillawa sama a wannan lokaci kuma za a ci gaba da samun haka.
A karshe ya ce har yanzu wasu ƙasashe basu kai kololuwar yaɗuwar annobar ba saboda haka ma a saurari karin alkaluman yawan wadanda zasu kamu a duniya.