Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 675 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litinin sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 288, Oyo – 76, Rivers – 56, Delta – 31, Ebonyi – 30, Gombe – 28, Ondo – 20 Kaduna – 20, Kwara – 20, Ogun – 17, FCT – 16, Edo – 13, Abia – 10, Nasarawa – 9, Imo – 9, Bayelsa – 8, Borno – 8, Katsina – 8, Sokoto – 3, Bauchi – 3 and Plateau – 2
Yanzu mutum 20,919 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 7109 sun warke, 525 sun rasu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum, 8, 864 , Sai babban birnin tarayyar Najeriya da ke da 1,583, Kano – 1,190, Oyo – 988, Rivers – 930, Edo – 797, Ogun – 663, Kaduna – 600, Delta – 532, Gombe – 479, Borno – 476, Bauchi – 467, Katsina – 434, Jigawa – 317, Ebonyi – 264, Plateau – 253, Imo – 243, Abia – 232, Nasarawa – 193, Kwara – 200, Sokoto – 138, Ondo – 154, Bayelsa – 177, Enugu – 144, Zamfara – 76, Kebbi – 67, Anambra – 66, Niger – 66, Yobe – 56, Osun – 60, Akwa Ibom – 65, Adamawa – 45, Benue – 44, Ekiti – 35, Taraba – 18, Taraba – 18, and Kogi – 3.
Hukumar NCDC ta gargadi mutane da su kula da tsoffi musamman wadanda ke fama da rashin lafiya kamar Asma, ciwon siga da dai sauran su. Hukumar ta ce likitoci sun shaida cewa lallai irin wadannan tsofaffi sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar.
Haka zalika, idan ba a manta ba, gwamnan Jigawa Mohammed Badaru ya shaida cewa jihar ta sallami duka wadanda suka kamu da cutar.
Gwamna Badaru ya ce mutum daya ne tal ya rage a jihar bai warke ba tukunna.
Discussion about this post