KORONA: Filato 31, Kaduna 28, Barno 2, Najeriya ta zarce mutum 20,000 da suka kamu

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 436 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Lahadi.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 169, Oyo – 52, Plateau 31, Imo – 29, Kaduna – 28, Ogun – 23, FCT – 18, Enugu – 18, Bauchi – 17, Bayelsa – 14, Rivers – 8, Osun – 6, Kano – 6, Edo – 5, Benue – 5, Adamawa – 3, Borno – 2, Abia – 1 da Ekiti – 1.

Yanzu mutum 20,244 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 6,879 sun warke, 518 sun rasu.

Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum, 8, 576, sai AbujaKORINA– 1,567, Kano – 1,190, Oyo – 912, Edo – 784, Rivers – 874, Ogun – 646, Kaduna – 580, Borno – 478, Gombe – 451, Bauchi – 464, Katsina – 426, Delta – 502, Jigawa – 317, Ebonyi – 234, Plateau – 251, Imo – 234, Abia – 222, Nasarawa – 184, Kwara – 180, Sokoto – 135, Ondo – 134, Bayelsa – 169, Enugu – 144, Zamfara – 76, Kebbi – 67, Anambra – 66, Niger – 66, Yobe – 56, Osun – 60, Akwa Ibom – 65, Adamawa – 45, Benue – 44, Ekiti – 35, Taraba – 18, Taraba – 18, da Kogi – 3.

Hukumar NCDC ta gargadi mutane da su kula da tsoffi musamman wadanda ke fama da rashin lafiya kamar Asma, ciwon siga da dai sauran su. Hukumar ta ce likitoci sun shaida cewa lallai irin wadannan tsofaffi sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar.

Haka zalika, idan ba a manta ba, gwamnan Jigawa Mohammed Badaru ya shaida cewa jihar ta sallami duka wadanda suka kamu da cutar.

Gwamna Badaru ya ce mutum daya ne tal ya rage a jihar bai warke ba tukunna.

Share.

game da Author