Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 348 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 163, FCT – 76, Ebonyi – 23, Rivers – 21, Delta – 8, Nasarawa – 8, Niger – 8, Enugu – 6, Bauchi – 5, Edo – 5, Ekiti – 5, Ondo – 5, Gombe – 5, Benue – 4, Ogun – 2, Osun – 1,Plateau – 1, Kogi – 1 and Anambra – 1.
Yanzu mutum 11166 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 3329 sun warke, 315 sun mutu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Jihar Legas na ci gaba da samun daruruwan mutanen da suka kamu da cutar Korona babu kakkautawa.
A ranar Talata kawai, jihar Legas ta samu karin mutum sama da sama da 142 da ya ninka jimlar yawan sauran jihohi 13 da suka samu karin wadanda suka kamu. Akalla jihohi 14 sun samu karin mutanen da suka kamu da kwayoyin cutar a ranar Talata.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 5, 440 , sai jihar Kano – 970, FCT – 763, Katsina – 371, Edo – 341, Oyo – 317, Kaduna – 297, Borno – 296, Ogun – 282, Jigawa – 274, Rivers – 249, Bauchi – 246, Gombe – 169, Sokoto – 115, Kwara – 111, Plateau – 109, Delta – 106, Nasarawa – 88, Zamfara – 76, Ebonyi – 63, Yobe – 52, Osun 47, Akwa Ibom – 45, Adamawa – 42, Niger – 41, Imo – 39, Kebbi – 33, Ondo – 33, Ekiti – 25, Enugu – 24, Bayelsa – 21 Taraba – 18, Abia–15, Benue – 13, Anambra – 12, and Kogi – 3
Discussion about this post