KORONA: Cikin kwana biyu Najeriya ta samu karin mutum sama da Dubu daya, Kaduna 14, Kano 5, yanzu mutum 13, 873 suka kamu

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 409 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 201, FCT – 85, Delta – 22, Edo – 16, Nasarawa – 14, Borno – 14, Kaduna – 14, Bauchi – 10, Rivers – 9, Enugu – 5, Kano – 5, Ogun – 4, Ondo – 4, Baylesa – 2, Kebbi – 2 and , Plateau – 2.

Yanzu mutum 13,873 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 4,351 sun warke, 382 sun rasu.

Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 6,266, sai jihar Kano – 1,025, FCT – 1,064, Ogun – 475, Edo – 478, Rivers – 403, Katsina – 399, Oyo – 398, Kaduna – 383, Borno – 367, Bauchi – 374, Jigawa – 309, Gombe – 246, Delta – 175, Ebonyi – 152, Kwara – 143, Sokoto – 129, Plateau – 129, Nasarawa – 127, Abia – 97, Imo – 83, Zamfara – 76, Yobe – 52, Osun 50, Niger – 46, Anambra – 46, Ondo – 50, Akwa Ibom – 45, Kebbi – 43, Adamawa – 42, Enugu – 35, Ekiti – 30, Bayelsa – 32, Taraba – 18, Benue – 13, da jihar dake da Kogi – 3.

Share.

game da Author