Ma’aikatar aikin haji ta kasar Saudi Arabiya ta sanar cewa baki ba za su halarci kasar domin yin aikin Haji a bana ba.
Ma’aikatar tace wadanda ke zaune a kasar ne kawai zau yi aiki tare da ‘yan kasar Saudiyya amma ba bu baki da ga wasu kasashe da za su shigo kasar domin yin aikin Haji.
Sanarwar ya kara da cewa gwamnatin Saudiyya ta yanke wannan hukunci ne a dalilin ci gaba da yaduwar annobar Korona sannan har yanzu ba a samu maganin ta ba.
Mahukunta sun ce aikin hajjin bana wato ta shekarar 1441 H/ 2020 za ayi da mutanen da ke zaune a kasar ne kawai wadanda dama acan suke zama, kasar Saudiyya. Amma babu baki daga wasu kasashe da za a bari su shigo.
Sannan kuma tace za a yi aikin ne tare da bin duk wasu hanyoyi da ka’idoji da aka zayyana na kare mutane daga kamuwa da wannan annoba ta Korona
Za a bayar da tazara yayin da ake aiki sannan kuma za a gudanar da shi kamar yadda addinin musulunci ya shar’anta kuma aka saba.